Daily Trust Aminiya - ‘Abin da ke kawo rikicin kabilanci a Najeriya’
Subscribe
Dailytrust TV

‘Abin da ke kawo rikicin kabilanci a Najeriya’

A ‘yan kwanakin nan, an samu rikice-rikice masu nasaba da kabilanci a yankin Kudu Maso Yammacin Najeriya.
Kama daga hare-hare a kan gidaje da dukiyoyin Fulani zuwa ga rikicin ‘yan kasuwa Hausawa da Yarabawa, wadannan lamura sun haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.
Hajiya Khadija Gambo Hawaja, mai rajin wayar da kan al’umma game da hanyoyin kauce wa munanan tashe-tashen hankula, ta bayyana wasu dalilan da ke haddasa irin wannan hatsaniya da hanyoyin magance su.