✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ke kawo yawan sakin aure a Arewacin Najeriya

A Arewacin Najeriya yawan sakin aure na da matukar tayar da hankali musamman a tsakanin matasa ma’aurata. Annabi Muhammad (SAW) ya bayyana ce duk mai…

A Arewacin Najeriya yawan sakin aure na da matukar tayar da hankali musamman a tsakanin matasa ma’aurata.

Annabi Muhammad (SAW) ya bayyana ce duk mai son ya samu kwanciyar hankali a aure to ya auri mai tarbiya, mai hali mai kyau saboda mata masu addinni su ne nasiha ke tasiri a kansu; Shi kuma namiji mai addini ko da soyayya ta kare to zai ji tausayin mace saboda tsoron da yake wa Allah.

A kan haka ne  Aminiya ta tattauna da wani masani kan zamantakewar aure, Anas Muhammad Dangana, inda ya bayaya cewa yawan sakin aure a Arewacin Najeriya ya samo asali ne daga dalilai kamar haka:

— Kwadayin iyaye

A yanzu yawancin iyaye idanunsu sun rufe da kwadayi da son abin duniya.

Hakan ya sa ba sa bincike a kan wanda za su bai wa  auren ’yarsu, in dai yana da kudi to shi ke nan ba ruwansu da dabi’unsa, kamalarsa, ko cancantarsa.

— Auren dole

Wani abin da ke kawo saki shi ne auren dole, domin wadansu iyayen ba sa la’akari da cewa ’ya’yansu naso ko basa son wanda za a aura musu; Kawai sai su aurar da su ga wadanda ba sa so. Daga karshe saki ya biyo baya.

— Karancin ilimi a kan aure

Akwai kuma karancin ilimi a kan auren da kuma rashin sanin darajarshi.

Yawancin masu aure ba su dauke shi a bakin komai ba, domin a tunaninsu in dai suna da kudi za su iya yin abin da suke so, su auri mata ko nawa ne.

Sannan rashin samun fadakarwa a kan zamantakewar aure shi ma illa ce babba, saboda wasu auren kawai suke yi, ba tare da sun san yadda ake zaman auren ba.

Kawai aboki ya yi, shi ma dole sai ya yi.

— Gazawa da biyan bukatun juna

Akwai kuma gazawa da biyan bukatun juna da nuna so kamar yadda ake a waje bayan an yi aure.

Idan miji ba ya iya biya wa matarsa bukatunta da kuma sauke hakkokinta a kanshi, hakan zai haifar da rashin jituwa a tsakaninsu da kuma rashin nuna soyayya kamar a farko.

— Daukar surutu da jita-jitar mutane

Idan kuma ma’aurata na biye wa surutan mutane da jita-jita, to tabbas aurensu ba zai dade ba, musamman idan suna boyon sirri wa junansu. Ko kuma su rika fadar matsalar cikin gidansu ga kawayensu ko wasu a waje.

— Rashin hakuri a tsakanin ma’aurata

Rashin hakuri a tsakanin ma’aurata yakan kawo rashin fahimtar juna, rashin yi wa juna uzuri da kuma saurin mutuwar aure.

— Karya kafin aure

Sannan yi wa juna karya kafin aure yana kawo mutuwar aure.

Wasu mazan za su iya yin komai don su mallaki mace, su yi mata karyar arziki duk saboda su samu su  a aure ta.

Idan kuma mace ta je gidansa bayan aure ta ga ba hakan ba ne sai a dinga samun sabani, daga nan za a iya samun matsala da za ta iya kaiwa ga rabuwar aure.

— Matsa wa ’ya’ya su fitar da miji

Matsa wa ’ya’ya mata a kan su fitar da mijin aure zai iay sa su tsaida wanda bai dace ba; Daga karshe a rika samun matsala a auren.

A karshe malam ya ja hankalin cewa a addinance an halatta idan zaka saki matarka ka bata wasu kudade da zatayi amfani dasu ta rike kanta, amma saboda rashin tsaurara hakan yasa basa jin bauyin sakin matansu saboda sunsa zasu sake auro wasu.