✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da nake son sauyawa a Kannywood —Stella Dadin Kowa

Ta bayyana abubuwan da suka shafi rayuwarta, kudirinta na kawo sauyi a Kannywood da sauransu.

Beatrice Williams Auta, jaruma ce a Masana’antar Kannwood, wadda ta taka rawar Stella a cikin shirin ‘Dadin Kowa’ mai dogon zango na tashar Arewa24.

A tattaunawarta da Aminiya, ta bayyana abubuwan da suka shafi rayuwarta da kudirinta na kawo sauyi a Kannywood da sauransu:

Mene ne takaitaccen tarihinki?

Sunana Beatrice Williams Auta, wadda aka fi sani da Stella a cikin shirin Dadin Kowa.

An haife ni a Jihar Kaduna, amma ’yar asalin Jihar Taraba ce. Na yi karatun firamare da sakandare a Kaduna, daga nan na wuce Jami’ar Jihar Kaduna inda na karanci Harshen Ingilishi da Wasan Kwaikwayo.

Iyayenmu mu biyu mata suka haifa, mahaifinmu ya rasu, amma mahaifiyarmu na raye.

 

Me ya ja hankalinki kika shiga harkar fina-finan Hausa?

Saboda ni ’yar Arewa ce kuma ina magana da harshen Hausa ne.

Na zabi fim din Hausa ne don fadakarwa da nishandarwa da wayar da kan al’umma ta wannan harshe.

Lokacin da nake yarinya ina matukar sha’awar fina-finan Indiya. Yadda suke rawa da sauran al’adunsu na birge ni.

To, idan ka kalli fim din Hausa za ka ga suna kama ta wasu fuskokin al’adu, shi ya sa kawai na zabi fim din Hausa.

 

Yaushe kika fara fitowa a fim?

A shekarar 2017.

 

Wanne ne fim dinki na farko?

Fim din Dadin Kowa.

 

Zuwa yanzu fina-finai nawa kika fito?

Ina tunanin adadinsu zai kai 10 zuwa 15 yanzu.

 

Kina da aure?

Magana ta gaskiya ban cika son tattauna abin da ya shafi rayuwata ba.

 

Wadanne jarumai ne suka fi birge ki a Kannywood?

A maza akwai Adam A. Zango da Ali Nuhu, a mata kuma akwai Rahama Sadau da Nafisa Abdullahi.

 

A baya-bayan nan an samu matsaloli da dama a Kannywood, me kike tunanin ya janyo faruwar haka?

Kannywood dai ta kasance cikin matsaloli da yawa, amma na fi tunanin hakan na da nasaba da yadda ake shirya fim din ba a kan tsarin da ya dace ba.

Sannan akwai matsalar rashin masu sanya kudadensu a cikin harkar; don haka shi ya sa ake kasa samun nagartattun kayan aiki.

Sannan akwai bangaranci ko son rai wajen zaben jaruman da za su taka rawa a fim, wanda hakan yana kawo koma baya ga manasan’antar, don haka ina tunanin wadannan ne ke jawo matsalolin. 

 

Kina daya daga cikin manyan jarumai a cikin shirin Dadin Kowa lokaci guda sai aka daina ganin ki, ko akwai wani dalili na faruwar haka?

Haka ne an daina gani na, ni kaina ba zan ce ga dalili ba, watakila a haka labarin ya zo, ba mamaki a gaba in sake fitowa, amma ba ni da tabbas.

 

Akwai jita-jitar cewa wadansu jarumai na shirin Dadin Kowa sun samu matsala da Hukumar Gudanarwar Arewa24, wanda hakan ne ya sa aka cire su daga shirin, me za ki ce game da haka?

Kamar yadda ka ce jita-jita, amma babu tabbacin hakan, amma ni kaina ba ni da wata matsala da Hukumar Gudanarwar Arewa24, daga bangarensu ban sani ba ko suna da matsala da ni, don na san na yi abin da suka bukata daga gare ni yadda ya kamata.

 

Me kike nufi da  ba ki sani ba ko suna da matsala da ke ba?

Ba ni da tabbaci, saboda a masana’anta za ka samu wani ba ya son ka kuma babu wani dalili, wani za ka ga yana sonka har yake ma alfarma, don haka ba wai ina nufin akwai wata matsala ba ce.

 

Kina tunanin siyasa ta ba da gudunmawa wajen samun rarrabuwar kai a Kannywood?

Duk wani rikici da za ka gani a duniya sai ka ga yana da nasaba da siyasa.

Ita siyasa aba ce ta bukata, kuma akwai mutane da dama daga Masana’antar Kannywood da ke da wata bukata ta daban.

 

Ana jita-jitar cewa daga cikin jaruman Kannywood akwai ’yan luwadi da ’yan madigo, kin taba cin karo da haka?

Wato kusan ko yaushe za ka rika jin jita-jita kan abubuwa da yawa, ni kaina na samu labarin haka amma magana ta gaskiya ban taba cin karo da wani ko wata wanda yake aikata haka ba.

Akwai wani kalubale da kike fuskanta a Kannywood ganin ke ba Bahaushiya ba ce?

Tabbas akwai kalubale ba kadan ba.

 

Wadanne kalubale kike fuskanta?

Da farko dai akwai addini da kuma matsalar kabilanci.

Wadansu daga cikin masu shiryawa na ganin idan ba za ka iya furta Hausa yadda ya kamata ba, kamar ba za ka iya ba su abin da suke bukata ba.

Kamar akwai wata Hausa da ake son amfani da ita a Kannywood.

Duk da cewar dukkanmu ’yan Arewa ne amma suna ganin akwai wata Hausa da sai ka iya ta sannan za a dama da kai.

Don haka wadannan su ne kadan daga cikin matsalolin da nake fuskanta.

 

Za ki iya auren dan fim?

Me zai hana? Ai a nawa tunanin wannan zai fi zama abin birgewa.

 

Ko kina da wani a Kannywood da kike son aura?

Wannan sirri ne, idan lokaci ya yi za ku ji.

 

Ko za ki iya ba mu satar amsa a kan wanda kike so?

Abin da zan iya cewa dogo ne, ai na ba ka satar amsar ko?

 

Idan aka ba ki matsayi a Kannywood, wace matsala za ki iya magancewa?

Da farko zan samar da hadin kai a cikin Kannwood. Wato a samu hadin kai a tsakanin masu shriyawa, ba da umarni, jarumai da kuma sauran masu ruwa-da-tsaki a harkar fina-finan Hausa.

Sannan zan yi kokarin samar da hadin gwiwa tsakaninmu da masana’antar fina-finai ta Nollywood, don ganin mun wuce matakin da muke a yanzu.

Kazalika, zan rika shirya horo ga ’ya’yan Masana’antar Kannywood don samar da ingantattun fina-finai, don a zahirin gaskiya muna da wuraren shirya fim masu kyau.

Mene ne babban burinki a Kannywood?

Ina kokarin gina kaina a yanzu don zama da kafata, kuma nan ba da jimawa ba zan fara shirya fina-finai nawa na kaina, wanda da haka nake fatar Allah Ya ba ni ikon zama daya daga cikin manyan jarumai mata a Kannywood.