✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abin da sakin Nnamdi Kanu zai haifar a Najeriya — CNG ta gargadi Buhari

Kar ya sake Buhari ya biye wa bukatar dattawan al’ummar Ibo.

Gamayyar Kungiyoyin kare yankin Arewacin Najeriya, CNG ta yi fatali da bukatar da aka gabatar wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na neman sakin jagoran haramtacciyar kungiyar ’yan awaren Biyafara ta IPOB, Nnamdi Kanu.

A Juma’ar makon da ya gabata ce wasu dattawan al’ummar Ibo suka ziyarci Buhari a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, babban birnin kasar, inda suka nemi alfarmar sakin Nnamdi Kanu.

Bukatar wadda Buhari ya kira mai girman gaske, ya sha alwashin cewa zai yi nazari a kanta.

Sai dai CNG ta bayyana bukatar a matsayin wani yunkuri na kawo cikas a bangaren shari’a, inda ta bayyana wadanda suka gabatar da ita a matsayin wadanda ana daukarsu a masu daukar nauyi da goyon bayan ta’addanci da laifuffukan da Nnamdi Kanu ya aikata a kasar.

Cikin hirar da ya yi da manema labarai ranar Litinin a Jihar Kano, Kakakin CNG, Abdulazeez Suleiman, ya soki martanin da Buhari ya mayar wa da dattawan al’ummar Ibo.

A cewarsa, “Arewa za ta dora wa Buhari alhakin jinin al’ummarta da aka zubar a sakamon ayyukan Kanu muddin ya kuskura ya mika wuya ga matsin lambar da ake masa kan sakinsa.

Suleiman ya ce, binciken da CNG ta gudanar a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, ya nuna cewa daga shekarar 2017 zuwa 2020, IPOB a karkashin jagorancin Nnamdi Kanu ta salwantar da rayukan ’yan Arewa 1,230 da ke zaune a yankin.

Kazalika, Suleiman ya ce Kanu da magoya bayansa sun salwantar da dukiyar miliyoyin kudi ta ’yan Arewa mazauna yankin a tsawon wannan lokaci.

CNG ta ce “la’akari da bukatar da dattawan al’ummar Ibo suka gabatar wa Shugaba Buhari da kuma alwashin da ya sha na yin nazari a kan bukatarsu, ya nuna cewa neman haddi a kan rayuwar dubban sojoji da ’yan sanda da sauran al’umma da ’yan awaren Biyafara suka salwantar zai tashi a wofi kenan.

“Martanin da Buhari ya mayar wa da dattawan al’ummar Ibo kan bukatarsu ya nuna cewa hakan goyon baya ne kan yadda ’yan awaren za su ci gaba da tara makamai da aka kawo musu daga ketare wanda tun ba yanzu ba ake amfani da su wajen tayar da tarzoma a kasar.

Suleiman ya ce, a kan haka ne CNG ta yanke shawarar cewa duk wani yunkuri na sakin Nnamdi Kanu zai mayar da kasar nan marar kiyaye doka da oda, inda take kira a kan kada Buhari ya biye wa bukatar dattawan al’ummar Ibon.

Haka kuma, Suleiman ya ce CNG tana gargadin Shugaba Buhari a kan kada ya manta da shamakin da ke tsakanin nauyin da rataya a wuyansa a matsayinsa na Shugaban Kasa da kuma nauyin da rataya a kan bangaren shari’a, wanda kowanne bangare na da iyakakokinsa.