✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abin da tsadar burodi ta haifar a jihar Kano

Malam Umar Adamu ya bayyana cewa a yanzu haka ya daina sayen burodi saboda tsadar da ya yi.

A kwanakin baya ne kungiyar masu yin burodi a fadin kasar nan suka bayar da sanarwar karin kudin burodi, lamarin da suka ce ya zama dole sakamakon tashin kudin wasu kayayyakin da ake hada burodin da su. 

Tun daga wancan lokaci da aka yi karin al’ummar Jihar Kano da dama suka kaurace wa sayen burodin kamar yadda binciken Aminiya ya gano.

Malam Umar Adamu ya bayyana wa Aminiya cewa a yanzu haka ya daina sayen burodi saboda tsadar da ya yi.

“Ina da iyalan da suka kai goma sha wanda a baya nakan sayi burodin Naira 700 ya ishe mu karya kumallo amma yanzu sai na sayi burodin Naira 1200 sanann ya ishe mu.”

Hakan ya sa na ajiye batun yin karin kumallo da burodi, sai muka koma yin fanke ko dafa taliya zuwa makaroni, domin wannan hanyar ce kadai za ta iya gamsar da iyalina.

Shi ma wani magidanci da Aminiya ta tattauna da shi mai suna Alhaji Ibrahim Isa, ya ce karin kudin burodin ya janyo ba kullum suke sayen burodi don karin kumallo ba.

“Ban daina cin burodi kwata-kwata ba, illa dai na rage sayensa. Kasancewar ’ya’yana suna son burodi ba zan iya soke cin burodi gaba daya ba saboda sun saba.

Ni ma idan gari ya waye idan ba burodi na ci ba, ba na jin dadi. A da kullum sai na sayi burodi amma a yanzu ba koyaushe nake saye ba. Wata rana sai mu hada da koko da kosai da wani abincin daban,” inji shi.

Wani mai shayi da Aminiya a tattauna da shi mai suna Malam Amadu Maishayi da ke Unguwar Mandawari ya ce a halin yanzu cinikin burodi ya yi kasa inda mutane suka fi sayen taliyar Indomi.

“Gaskiya ciniki ba kamar baya ba domin yanzu mutane sun fi sayen indomi da kwai a kan burodi don a cewarsu sun fi koshi idan suka ci indomi,” inji shi.

Alhaji Kabiru Hassan shi ne Jami’in Hulda da Jam’a na Kungiyar Masu Burodi ta Kasa, kuma shi ne Sakataren Kungiyar ta Jihar Kano ya shaida wa Aminiya cewa a tashin farashin burodin ya kawo koma baya a harkar burodin gaba daya.

“Gaskiya hakan ya shafe mu domin a halin da ake ciki mai yin burodin fulawa buhu biyar a da to yanzu uku yake iya yi saboda babu ciniki sosai.”

Sai dai a cewarsa duk da tashin farashin da burodin ya yi har yanzu yana daga cikin abinci mai saukin saye da kuma sarrafawa.

“A cikin kayan abinci burodi ne kadai mutum zai iya sayen na Naira 100 ya ci ya koshi kuma zai iya cin sa a haka ba tare da ya nema masa mahadi ba.”

“Idan mutum ya ci ya sha ruwa shi ke nan bukata ta biya, don haka duk da tashin farashin da ya yi har yanzu yana da sauki a kan nau’o’in wasu abincin,” inji shi.