✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba za mu fallasa masu taimakon ’yan ta’adda ba —Gwamnati

Ministan Shari'a Abubakar Malami ya ce akwai dokar fallasa wadanda ake zargi.

Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya ce Gwamnatin Tarayya ba za ta fallasa sunayen mutanen da ake zargi da tallafa wa ayyukan ta’addanci da kudade ba.

Malami ya bayyana haka ne a lokacin da ya ce gwamnatin Najeriya tana bibiya, ta kuma gano wadanda ke taimaka wa ayyukan ta’addanci da kudade, ta rufe asusun ajiyarsu, tana kuma kan gudanar da bincike da ke haifar da kyawawan sakamako.

“Abin da Gwamntanin Tarayya ta yi na rashin bayyana suna da kuma kunyata wadanda ake zargi da daukar nauyin ayyukan ta’addanci shi ne bin kundin tsarin mulki da ya hukunta daukar kowane mutum a matsayin mara laifi.

“Abin da doka ta tanadar shi ne idan aka tashi gurfanar da mutum a gaban kotu za a bayyana sunansa, kunyata shi kuma abu ne da zai biyo baya idan har an kama shi da laifi” inji ministan shari’ar.

Ya kara da cewa, “A taikace batun bayyana suna ko kunyata masu laifi na da ka’ida a kundin tsarin mulki, domin yana farawa ne da gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu, sannan ya kare idan an sami mutumin da laifi — Ba duk yadda aka ga dama ake yin sa ba.”

Ya yi bayanin nasa ne gabanin Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 76 da ke gudana a Birnin New York na kasar Amurka.

Malami ya ce Ofishin Binciken Laifuka na Kasa ya binciki kundaye sama da 1,000 na tuhume-tuhume da ake wa masu taimaka wa ayyukan kungiyar Boko Haram, wadanda daga cikinsu aka gurfanar da 285 a gaban kotu, bisa hujjojin da aka samu a kansu.

A cewarsa, bullar cutar COVID-19 da yajin aikin kungiyar lauyoyi da ma’aikatan shari’a na daga cikin abubuwan da ke kawo tafiyar hawainiya a shari’ar wadanda ake zargi da taimaka wa ayyukan ta’addanci.

Malami, ta sanarwar da mai magana da yawunsa, Umar Jibrilu Gwandu, ya fitar ya ce, gwamnati ta toshe kofofin taimaka wa ’yan ta’adda da kudade.

“Gaskiyar ita ce muna ci gaba da gudanar da bincike, amma ba zan bayyana abin da ake ciki ba, saboda hakan na iya yi wa shari’a karan tsaye.

“Amma duk abin da muke yi, tun daga kamawa har zuwa tsare wadanda ake zargi, muna yi ne daidai da abin da kundin tsarin mulki ya tanada,” inji sanawar ta Gwandu.