✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Abin da ya hana mu zuwa jana’izar Inuwa Abdulkadir’

Shugabannin reshen Jihar Sakkwato na APC sun ce ba da gangan suka ki halartar jana’izar tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na Arewa Maso Yamma, marigayi Barista…

Shugabannin reshen Jihar Sakkwato na APC sun ce ba da gangan suka ki halartar jana’izar tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na Arewa Maso Yamma, marigayi Barista Inuwa Abdulkadir.

Rashin ganin jagororin jam’iyar na jihar Sakkwato yayin janazar dai ya ja hankalin mutanen da suka halarci wurin ganin ko ba komai yana cikin shugabanninsu na kasa a lokacin rayuwarsa.

Shugaban jam’iyar APC na jihar Sakkwato Alhaji Isah Sadik Achida ne ya yi bayani game da rashin ganinsu, duk kuwa da cewa magoya bayan jam’iyyar PDP da shugabanninsu sun halarci wurin.

“Wannan abin da ya faru ba da gangan ba ne, ba don muna da matsala da wani ba ne, a lokacin da abin ya faru jagororinmu Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko da Ahmad Aliyu Sokoto da  Minista Muhammad Maigari Dingyadi duk suna Abuja,” inji Alhaji Sadik Achida.

Shugaban ya ci gaba da cewa shi kuma a lokacin da abin ya faru mahaifiyar amininsa ce ta rasu suna wurin yi mata sutura don haka ne bai je ba.

“Muna yi masa rokon Allah Ya gafarta masa Ya sa ya huta, ba mu da wata matsala da kowa,” inji Achida.

Al’ummar Jihar Sakkwato dai sun ga laifin jagororin saboda rashin ganinsu a wurin jana’izar kuma ba a ga wata tawaga da ta fito daga jam’iyar ba – baya ga dan Majalisar Wakilai mai wakitar kananan hukumomin Gwadabawa da Illela kusan ba wani jigo a jam’iyar da aka gani.

Tsohon mataimakin shugaban na APC ya rasu yana da shekara 54 a duniya, kuma ya bar matan aure biyu da ’ya’ya tara.