✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya kamata masu kallonmu su rika yi mana — Shehu Hassan Kano

To, ai shi fim rai ke gare shi, ma’ana yana tafiya ne da rayuwa.

Alhaji Shehu Hassan Kano tsohon Shugaban Kungiyar Jaruman Masana’antar Kannywood da ke Kano ne kuma daya daga cikin ’yan Kwamiti Amintattun Kungiyar.

A zantawarsa da Aminiya a Kalaba, ya yi tsokaci game da zargin masu shirya fina-finan Hausa da sakin layi wajen yin fina-finan da suke nuna hada-hadar miyagun kwayoyi da kwacen waya da sauransu.

Shehu Hassan wanda wasu ke kira ‘Tindirki’ ya ce ba manufarsu bata tarbiyya ko a yi koyi da mugun aiki ba ne, a’a suna ankarar da jama’a ne kan yadda zamani ya sauya don kowa ya ankare:

Kwanan baya Hukumar Tace Fina-Fina ta Jihar Kano ta yi korafi kan yadda ake samun fina-finan da suke nuna yadda ake kwacen waya ko sayar da miyagun kwayoyi da sauran abubuwan da ta ce sun saba wa al’adar mutanen Arewa.

Me za ka ce?

To wannan al’amarin wani al’amari ne da dama can mun jima muna fama da shi, amma a kowane lokaci muna gaya wa abokan sana’a cewa a nemi ilimin wannan sana’a.

Mutane da dama kuma suna kokarin neman ilimin; masu rubuta labari da daukar hoto da duk wani abu da ake yi a wannan masana’anta mun yi sa’a mun samu aji na koyar da wannan sana’a, wannan al’amari ya sa idan masu kallonmu suna bin mu a hankali za su iya gani daga misalai, daga irin wadannan da ake yi yanzu irin su ‘Labarina,’ kamar ‘Kwana Casa’in’ za a ga cewa an samu bambanci da irin tafiyar da ake yi a wancan lokaci.

Yanzu wani lamari ne ya riga ya ba mutane wata hanya daban ta tattaunawa da muhawara a kan abubuwan da ake gabatarwa.

Ka ga harkar ilimin ta yi amfani kuma a kanta ake har yanzu.

Bayan neman ilimin sana’ar wane bangare za ku duba domin yin gyara?

To, ai shi fim rai ke gare shi, ma’ana yana tafiya ne da rayuwa, duk abubuwan da suke tafiya a rayuwa, su ake kallo su ake dauka, su ake kwaikwaya.

Wannan ya sa a tunanina in muka samu labarin an yi shi yana cutarwa, za mu kira masu shi, mu sa su gyara.

Don haka, wannan ya nuna a shirye muke idan rayuwa ta canja ta bangaren shugabanninmu da bangaren ’yan siyasarmu da bangaren sarakunanmu, duk irin abubuwan da muka gani na alheri da za su ciyar da mutane gaba, to, su muke dauka mu kara nunawa a fim domin a kara gane manufarsu da inda suka sa gaba.

Wanda suka yi na son zuciya ko na batawa, za mu dauke shi mu canja mu nuna wa mutane domin su gane cewa irin salon shugabancin da ake yi wato ana cutarwa.

Su irin wadannan fina-finan da ake nunawa ana nuna su ne don a fadakar da mutumin da ya zo daga dajin Karakande ya shigo birni ya gane ga yadda ake yi a kwace wa mutum waya, ga yadda za a yi a cutar da shi, ga irin salon da ake yi ana cutar da jama’a.

Kamar yadda na yi maka bayani don jama’a su kiyaye a kuma wayar da kai ga jami’an tsaro ga yadda ake cutar da jama’a.

Manufar wadannan fina-finan, ita ce a wayar wa jama’a kai a yi bayani ga al’ummar da ba su san yaya ake cutar da su ba da kuma wayar da kai ga jami’an tsaro kan yadda ake cutar da jama’a don su fitar da mutane daga cikin wannan bala’i.

Kana nufin karancin fahimta ta sa ake wannan fassara?

Kwarai da gaske, ai ka san akwai mutumin da za ka gani a cikin fim an nuna ga yadda ya damfari wani ya yi masa wata dabara irin ta ilimi, to kai magidanci wanda ka kalli irin wannan fim din, washegari idan ka ga wani ya zo da irin wannan shigar yana nema ya bi irin waccan hanyar ya cutar da kai, to, ka gani a fim ba za ka bari ka cutu ba.

Mene ne sakonka ga masoya fina-finanku?

Sakon kullum bai wuce masu kallon fina-finanmu su rika kallonmu da zuciya daya ba.

Abin da nake nufi da zuciya daya shi ne, Bahaushe ya ce duk mutumin da za ku yi mu’amala da shi, to, idan ka fara raina shi tun farko, kuma kake jin cewa akwai wani taimako da kake so ta wurinsa, babu shakka ba za ka taba ganin nagartarsa ba.

Amma idan masu kallon mu za su yi hakuri su rika kallonmu da zuciya daya, tabbas za su rika gane irin sakonnin da muke aikewa a cikin fina-finanmu.

Don haka sakona shi ne, kullum a kalle mu da ilimi da zuciya daya, sai kuma a fahimci inda muka nufa, in Allah Ya yarda za a ci gaba da gane sakon da yake cikin fina-finanmu.