✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa muka takaita hada-hada a Najeriya —Gwamnati

Hukumomi a Najeriya sun ce sun bayar da umarnin takaita hada-hada ne, musamman a biranen Abuja da Legas, a ci gaba da yunkurin dakile yaduwar…

Hukumomi a Najeriya sun ce sun bayar da umarnin takaita hada-hada ne, musamman a biranen Abuja da Legas, a ci gaba da yunkurin dakile yaduwar Coronavirus.

Yayin wani taron manema labarai ranar Litinin, Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha ya kuma ce hukumomin sun yanke shawarar rufe iyakokin kasar gaba daya—ma’ana ba sauran shiga ko fita.

Wata sanarwa da Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya Folashade Yemi-Esan ta fitar da maraicen ranar Litinin ta umarci kananan ma’aikata su zauna a gida.

“A matsayin wani karin matakin dakile yaduwar COVID-19, dukkan ma’aikatan gwamnatin da ayyukansu ba su zama dole ba wadanda ke matakin albashi na 12 zuwa kasa za su rika aiki daga gida tun daga ranar 24 ga watan Maris har sai abin da hali ya yi”, inji sanarwar.

Su kuwa ma’aikatan da za su je ofis, hukumomin sun bukace su da su takaita yawan mutanen da za su gana da su matuka.

Sanarwar ta kuma bukaci ma’aikatan da suka dawo daga kasashen da ke fama da cutar, ko suka yi mu’amala da masu dauke da ita, su killace kansu har tsawon mako biyu.

Daga cikin matakan da Sakataren Gwamnati Boss Mustapha ya sanar na hana yaduwar Coronavirus dai har da dakatar da taron mako-mako na majalisar ministocin kasar, wanda ake yi duk ranar Laraba, da dakatar da taron Majalisar Kasa wanda aka shirya yi ranar Alhamis.

Tuni dai hukumomi a matakai daban-daban suka ba da umarnin rufe makarantu kama daga kanana zuwa manya, sannan suka umarci mabiya addinai su takaita taruwar jama’a a wuraren ibada.

A wasu jihohin ma har jami’an tsaro aka yi amfani da su wajen tabbatar da aiki da wannan umarni.

Zuwa yanzu dai Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) ta ce mutum 40 ne aka tabbatar sun kamu da cutar a Najeriya.

Hukumar ta ce mutum guda ya riga mu gidan gaskiya yayin da aka salami wasu biyu bayan sun samu lafiya.