✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa aka tsere wa matan Hausawa a harkar kasuwanci

Abubuwan da suka sa matan Hausawa suke baya a harkar kasuwanci a yayin da takwarorinsu ke samun ci gaba.

Tarihin kasuwanci ba zai cika ba ba tare da an ambaci mata da suka yi fice a cikinsa ba. Misali, ba za a taba mantawa ba da Khadija, matar Annabi (SAW) wadda ’yar kasuwa ce.

Tun iyaye da kakanni babban abin da aka san Hausawa da shi shi ne noma, kiwo da kuma kasuwanci ko fatauci.

Wannan shi ya sa ake da fatake a kasar Hausa, wadanda kan yi bulaguro zuwa sassan nahiyar Afrika da kasashen Larabawa domin saye da sayarwa.

A dalilin haka ne aka samu Hausawa mazauna kasashe da yawa a nahiyar Afrika da kuma kasashen Larabawa.

A yayin da harkar kasuwanci yake ta bunkasa tare da sauya salo a Najeriya da ma fadin duniya, amma matan Hausawa na baya a wannan bangaren idan aka kwatanta su da takwarorinsu a kasar.

A kan haka ne Aminiya ta tattauna da wasu mata Hausawa kuma matasan ’yan kasuwa domin gano abubuwan da suke jawo tarnaki ga kasuwancin mata Hausawa.

Zamani ya canza al’amura

Sanin kowa ne cewa a da can kusan duk wanda ya yi karatun boko, mace ne ko namiji, yana da tabbacin zai samu aikin gwamnati ko na kamfani.

Amma yanzu al’amura sun canja, al’umma ta yi yawan da ba zai yiwu duk wanda ya yi karatun boko ya samu aikin gwamnati ko na kamfani, ballantana wanda bai yi ba.

Wannan ne ya sa gwamnati da kungiyoyi suke ta fadarkarwa a kan cewa a mayar da hankali wajen nema wa kai abin yi ba tare da dogaro da gwamnati ko wani mutum ba.

Binciken da Aminiya ta yi ya nuna duk da cewa akwai matan Hausawa da suka shiga gadan-gadan ana damawa da su a harkar kasuwanci, amma har yanzu a baya suke duk kuwa da cewa yanzu akwai hanyoyi masu yawa kuma masu sauki na saye da sayarwa musamman ta hanyar amfani da fasahar zamani.

Abubuwan da ke kawo cikas

Shin me ya sa matan Hausawa suke baya a daidai lokacin da takwarorinsu kuma a kasarsu suke zama fitattun attajirai?

A hirar da Aminiya ta yi da wata daliba a Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta Dutse kuma Shugabar Kamfanin Girke-girke na Mi’iraj Kitchen, A’isha Musa Ibrahim, ta ce matsalar kasuwancin matan Hausawa na da alaka da abubuwa biyu zuwa uku:

Al’ada

“A al’adar Bahaushe ita mace a gida aka san ta, kusan komai yi mata ake a matsayinta na ’ya, yaya, mata, uwa ko kaka.

“Ba kasafai ake ganin mace ta dogara ga kanta ba a kasar Hausa, galibi komai nata ya dogara ne a kan namiji,” inji ta.

Ta bayyana cewa, “Wannan ya sa da dama ba sa yin wani hobbasa wajen neman na kansu tun da komai yi musu ake sabanin sauran kabilu.”

Raina kananan sana’oi

Matashiyar ’yar kasuwar ta kara da cewa, “Da yawa daga cikin mata Hausawa suna raina karamar sana’a.

“Galibin kananan sana’o’i a garuwanmu ba matan hausawa ba ne ke yi.

“Matan sauran kabilu za su iya sayar da masara ko kosai, ta hakura da karamar riba don ta dogara da kanta. Dama da karami ake babba.

“Wannan na daga cikin manyan matsalolin da suka sa muke da rauni a harkar kasuwanci.

Rashin hakuri

“Haka kuma kamar komai na duniya, kasuwa ba ta yiwuwa dole sai da hakuri. Babu yadda za a yi maras hakuri ya samu nasara a kasuwanci.

“Dole ka harura da kadan ka domin kamar shuka bishiya ce, dole sai kin raine ta har zuwa girma sannan ki ci amfanin ’ya’yanta.

“Duk wani babban dan kasuwa da ka gani yau ko kake jin labarinsa, to ka tabbata da kadan ya fara, ya kuma raine shi har aka zo lokacin da yake cin amfanin shukar da ya yi.”

Ita kuma mai kamfanin Fareeda Collections kuma Daliba a Tsangayar Aikin Noma ta Jami’ar Gwmnatin Tarayya ta Dutse, Farida Abubakar, ta ce wannan matsalar na da alaka da abubuwa kamar haka:

Rashin Tallafi

“Galibin mata ba sa samun tallafi daga iyalansu kuma da yawansu ba su san yadda za su sami tallafin da gwamnati da kungiyoyi suke bayarwa ba.

“Wannan babban tarnaki ne domin shi kasuwanci dole sai da jari komai kankancinsa.

“Rashin samun taimako daga iyali kuma yana da nasaba da tunanin da wasu suke da shi na cewa mace ba ta da bukatar kudi saboda komai yi ma ta ake.”

Rashin bayar da muhimmanci

Matashiyar ’yar kasuwar ta ci gaba da cewa, “Shi kasuwanci abu ne da ke bukatar mayar da hankali da kuma ba shi muhimmaci.

“Yawanci matanmu ba sa mayar da hankali da kuma ba wa kasuwancinsu muhammanci sabanin sauran kabilu.

“Wadannan na daga cikin manyan dalilan da suka sa kasuwancin matan kasar Hausawa ke da rauni a daidai lokacin da duniya ta karkata zuwa kasuwanci da sama wa kai abin yi.