✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abin da ya sa aka umarci jihohi su dakatar da yin rigakafin COVID-19

Babu tabbacin isowar rukuni na biyun rigakafin Oxford-AstraZeneca da aka fara bayarwa a Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta bayyana dalilinta na umartar jihohi su dakata da yi wa mutane allurar rigakafin cutar COVID-19 na Oxford-AstraZeneca da zarar sun yi amfani da rabin wanda aka raba musu.

Minista a Ma’aikatar Lafiya, Olorunnimbe Mamora, ya ce bayar da umarnin dakatar yin allurar rigakafin ya zama wajibi saboda rashin tabbacin isowar rukuni na biyun rigakafin da aka fara a Najeriya.

“An yi hakan ne domin wadanda aka yi musu na farko su samu su kammala karbar rigakafin nasu.

“Kasancewar ba mu da tabbacin yaushe rukuni na biyu na rigakafin AstraZaneca zai iso Najeriya ba, abin da ya fi dacewa shi ne gara a karasa na wadanda aka riga aka fara yi musu,” inji shi a ranar Talata.

“Da haka ne,” a cewar Mamora ga taron hadin gwiwar Kwamitin Kasa kan Yaki da COVID-19, “za mu iya cewa akwai mutanen da aka riga aka kammala musu saboda sau biyu ake yin sa.

“Dalilin bayar da umarnin ke nan, maimakon a yi ta yi wa mutane sau daya alhali sai an yi sau biyu ake yi. Shi ya sa muka ce maimakon kawai a yi ta yi wa kowa, gara a tabbatar da cewa zuwa lokacin za a gama amfani da rigakafin da ake da shi a yanzu, duk wadanda suka samu an kammala yi musu,” inji shi.

A nasa bangaren, Darakta Janar na Cibiyar Kula da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC), Dokta Chikwe Ihekeazu, ya tabbata cewa NCDC na gudanar da bincike kan musabbabin aman jin da wata mata ta yi bayan an yi mata allurar rigakafin na AstraZeneca.

Shi ma da yake bayani, Shugaban Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Kasa (NPHCDA), Dokta Faisal Shuaibu ya bayyana cewa ba a yin gamin gambizar allurar rigakafin COVID-19 na AstraZeneca da na kamfanin Johnson and Johnson.

Ya ya bayanin ne a lokacin da yake amsa tambaya ko wanda ya fara karbar rigakain AstraZeneca zai iya karasawa da na Johnson and Johnson idan karashen na AstraZeneca ba sa mu ba.

“Ba daidai ba ne. Ba zai yiwa a yi wa mutum na AstraZeneca a hannun hagu sannan a yi masa na Johnson and Johnson a hannun dama ba. Dole ne ya kasance duk su kasance na AstraZeneca ne ko na Johnson and Johnson,” inji shi.

Game da wasu matsaloli da ake dangantawa da rigakain na AstraZeneca, ya ce , “Mun sha yin bayani cewa wadannan rigakafin da na wasu matsaloli, amma ba rigakafin COVID-19 kadai ne ke da matsalolin.”