✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa ake binciken Masarautar Kano kan badakalar filaye

Sai dai abin mamakin shine yadda wasu suka ce mutumin da ake zargi da yin dillanci zamanin tsohon Sarki Sanusi II shine dai yake da…

Wani sabon rikici ya barke tsakanin Masarautar Kano da Hukumar Karbar Korafe-Korafe da Yaki da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC) bisa zargin Masarautar kan wata badakala a sayar da wasu filaye.

Hakan dai nan zuwa ne shekara daya bayan Alhaji Aminu Ado Bayero ya dare kan karagar masarautar, bayan wanda ya gabace shi, tsohon Sarki Muhammadu Sanusi II shima ya fuskanci makamantan irin wadannan zarge-zargen.

A wannan karon dai ana zargin Sarki Aminu Bayero ne da sayar da filin da fadinsa ya kai kusan hekta 22 a Gandun Sarki dake unguwar Dorayi Karama a Karamar Hukumar Gwale tare da kartakatar da kudaden zuwa lalitarsa.

A wasu mabanbantan umarni da kotu ta bayar ranar 31 ga watan Maris da kuma daya ga watan Afrilun 2021 sun nuna cewa PCACC, wacce ita ce hukumar da ta binciki tsohon Sarki Sanusi II tana kuma binciken Sarki Aminu Bayero.

Da farko dai kotun ta dakatar da shugaban PCACC, Muhyi Magaji Rimin Gado da Mataimakin Babban Sufeton ’Yan Sanda na Shiyya ta daya “daga ci gaba da rusa gine-gine ko kuma yin katsa-landan ta kowacce hanya a kan kadarorin dake Dorayi Karama (wato Gandun Sarki) har sai lokacin da  za ta yanke hukunci a kan bukatar mai kara.”

Wanda ya shigar da karar, Alhaji Yusuf Shu’aibu Aliyu wanda ya sayi filayen daga Masarautar Kano ya kuma sami umarnin hana ci gaba da musguna masa a kokarinsa na gina ‘rukunin gidaje’ a wurin.

“Mun san suna yunkurin yin amfani ne da hutun bukukuwan Ista sakamakon babu aiki a ranakun Juma’a da Litinin domin ci gaba da aikin kafin mu sami umarnin kotun da zai dakatar da su,” inji wata majiya daga Sashen Shari’a na PCACC a hirarta da Aminiya.

Sai dai PCACC ita ma ta garzaya wannan kotun dake karkashin jagorancin Mai Shari’a Usman Malam Na’Abba, wato Babbar Kotun Kano dake kan titin Miller inda ta sami wani umarnin da ya dace da bukatarta kan dakatawa daga ci gaba da daukar kowanne irin mataki har zuwa lokacin da kotun za ta ci gaba da sauraron karar ranar 12 ga watan Afrilun 2021.

Aminiya ta gano cewa an raba filayen da ake takaddamar a kansu zuwa gida biyu; hekta takwas mallakin rukunin gidajen Marigayi Sarkin Kano Ado Bayero ne, yayin da hekta 14 kuma mallakin Masarautar Kano ne.

PCACC dai ta dakatar da aikin saboda binciken da take yi a kan tsahon Sarki Muhammadu Sanusi II saboda sayar da wasu kadarorin a unguwar Darmanawa.

Sai dai a ranar 22 ga watan Oktoban 2020, Gidauniyar dake kula da rukunin gidajen Ado Bayero Royal City dake unguwar Dorayi, mallakin marigayi Sarkin Kano Ado ta bukaci hukumar PCACC da ta janye daga dakatarwar da ta yi a kan gidajen ta kuma kyale ta ta ci gaba da aiki a kai.

Rahotanni sun nuna cewa wani Aliyu, wanda Kansila ne a Karamar Hukumar Birnin Kano da Kewaye ne ya sayi filayen guda 114 da kudinsu ya kai Naira miliyan 575 kuma ya biya kudin lakadan.

Hakan ne ya sa Kungiyar Ci Gaban Al’ummar Dorayi ta kai korafi zuwa PCACC tana bukatar a binciki yunkurin yin kaka-gida a kan filayen na unguwarsu.

Za mu yi zuzzurfan bincike a kai – PCACC

Shugabn hukumar PCACC, Muhyi Magaji Rimin Gado ya tabbatar da cewa hukumarsa za ta binciki Masarautar Kano da duk wanda ake zargi a cikin badakalar.

Da aka tambaye shi ko hukumar za ta gayyaci Sarkin na Kano sai ya ce a’a, ba yanzu ba.

Sai dai abin mamakin shine yadda wasu suka ce mutumin da ake zargi da yin dillanci zamanin tsohon Sarki Sanusi II shine dai yake da hannu dumu-dumu a wannan karon ma.

Sai dai duk kokarinmu na jin ta bakin Sarki ko kuma shi Alhaji Aliyun ya ci tura.

Duk kiran da muka yi wa Alhaji Aliyun da wanda muka yi wa Shugaban Ma’aikatan Fadar Sarkin, Alhaji Ahmed Ado Bayero ba a dauka ba kuma basu amsa rubutaccen sakonnin da aka aike musu ba.