✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa ba za mu gurfanar da tubabbun ’yan Boko Haram a kotu ba – Gwamnati

Gwamnatin ta ce yin hakan ya saba da tanade-tanaden kasa da kasa.

Gwamnatin Tarayya ta bayyana dalilin da ya sa ba za ta iya gurfanar da tubabbun ’yan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram a gaban kotu ba.

Ta ce yin hakan ya saba da tanade-tanaden kasa da kasa.

Ministan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakan yayin wata tattanauwarsa da ’yan jarida a birnin Washington D.C na kasar Amuraka ranar Juma’a.

Ya ce kiraye-kirayen da ake yi kan a gurfanar da tubabbun ’yan ta’addan ko kuma a kashe su a maimakon a yi musu a fuwa ya saba da tanade-tanaden kasa da kasa.

A cewarsa, “Ni da kaina na yi wa sojoji magana kafin na bar Najeriya inda suka shaida min cewa suna yin abin da dokokin kasa da kasa suka tanada kan wadanda suka mika wuya ko suka ajiye makamansu ana daukarsu ne a matsayin fursunonin yaki.

“Ba zai yuwu kawai ka bude musu wuta ba, akwai dokokin da suka ba fursunonin yaki ’yanci. Abin da sojoji suke yi shi ne idan suka mika wuya, za a dauki bayanansu domin tabbatar da cewa tuban na hakika ne ba tuban muzuru ba, kafin a sake karbarsu a cikin al’umma,” inji Ministan.

A ’yan kwanakin nan dai, mayakan Boko Haram da dama ne suka mika wuya ga sojojin Najeriya a yankin Arewa maso Gabas da ya jima yana fama da rikici.