✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abin da ya sa farashin kwai tashin gwauron zabo

'Za a ci gaba da samun karancin kwai har zuwa watan Afrilu'

Wata mai gidan kaji ta yi hasashen cewa za a ci gaba da samun karanci da kuma tsadar kwai har zuwa watan Maris ko Afrilu Najeriya. 

Folake Aina ta bayyana haka ne yayin da tashin gwauron zabon farashin kwai da kuma karancinsa ke kara sanya damuwa ga ’yan kasuwa da sauran masu gidajen gona.

Wani mai sayar da kwai ya bayyana wa Aminiya damuwa kan karancin kwai a makonnin baya-bayan nan wanda ya ce ya sa shi rasa kwastomomi.

Duk da cewa akan samu karin tsada ko karancin kwai a duk shekara, masu gidajen kaji da masu sayar da kwai na kokawa cewa yanayin na bana tattare da rashin tabbas.

Demola Adekunle ya ce a halin yanzu gidajen kajin da yake sayen kwai kiret 350 a duk mako sun daina aiki a ’yan makonnin nan.

Demola mai shagon sayar da kwai a yankin Oke-Afa a Legas ya ce tsadar abincin kaji ya tilasta daya gidan kajin da yake sayen kwai daina aiki, dayan kuma har yanzu bai sa ranar fara sayar da kwai ba.

Don haka ya ce kullum sai rasa kudaden shiga da kwastominsa yake yi domin ba shi da zabi face ya bayyawa wa kwastomomin cewa ba shi da kwai.

Tsahin gwauron zabon kwai

Wata mai sayar da kwai ta ce duk da tashin gwauron zabon da ya yi tana samun kwan ta saya.

Misis Bridget Stephen ta ce Yanzu farashin kiret din kwai da a baya ake sayarwa N950 ya koma N1,300 a Legas.

Abin da ya kawo tsadar kwai

Wata mai gidan kaji ta bayyana wa Aminiya abubuwan da suka haddasa karancin kwai da kuma tsadarsa.

Ta ce yawancin gidajen gonan sun riga sun sayar da kajinsu a  lokacin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara a watan Disamban 2020.

Folake Aina ta ce akan dauki wata uku zuwa hudu kafin da maye gurbin kajin da za su yi kwai.

Ta kara da cewa an samu tsadar kwai a 2021 ne sakamakon hauhawar farashin abincin kaji da ya sa manoma ba za su iya sayen ’yan tsaki ba da za su kiwata.

Folake ta ce kusan a duk mako sai abincin kaji ya kara kudi; duk da bude iyakokin Najeriya, ba a rage farashin masara da waken soya ba, kuma su ne manyan kayan hadin abincin kaji.

Sannan sinadaren hada abinci kajin daga kasashen kasashen waje ake shigo da su, ga shi kuma farashin Dala ya tashi tare da haifar da tashin farashin kayan hadin abincin kaji.

Ta ce bayan haka farashin alkama da ake nomawa a cikin gida ma ta tashi.

“Idan ma gwamnati ta taimaka a kan matsalar masara, waken soya da alkama, akwai kuma matsalar sinadaren hada abinci hada abincin.

Da sauran rina a kaba

“Idan ba N1,500 gidajen gona suke sayar da kiret din kwai ba, ba yadda za a yi su ji dadi,” inji ta.

Folake wadda ita ce Shugabar VD & T farm ta ce, “Na kan sayi ’ya’yan tsaki sannan in yi kiwon su na sati 12 zuwa 15.

A 2019 N1,250 ake sayarwa amma yanzu ya koma N1,650. Idan yanzu zan sayi ’ya’yan tsaki 1,000 karin ya kai N400,000, idan kuma 10,000 ne karin Naira miliyan hudu ke nan.

“Sannan sai an ciyar da su na wata biyu (sati 20) kafin su fara saka kwai. Matsalar da manoma ke fama da ita ke nan.

“Kudaden da masu kiwon kaji suka samu a lokacin bukukuwan karshen shekara ba za su cike gibin da ake bukata a wurin abincin kaji da kuma farashin ’ya’yan tsaki ba,” inji mai gidan kajin.

Ta yi hasashen cewa za a ci gaba da samun karanci da kuma tsadar kwai har zuwa watan Maris ko Afrilu, lokacin da kajin da aka zuba suka fara saka kwai.

Ta ce manoma ba sa zuba sabbin ’ya’yan tsaki sai bayan sun sayar da wadanda suke da su, sannan sai sabbin sun yi kusan sati 20 kafin su fara yin kwai.