✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa fim din Labarina ke daukar hankali

Abubuwan da suka sa fim din Labarina daukar hankali mutanen da ba a yi tunani ba

Sanarwar da daraktan fim din Labarina, Malam Aminu Saira ya yi cewa za a dakatar da nuna wasan kwaikwayon na wani lokaci da za a sanar da kafar da za a ci gaba da nunawa ya dagula wasu mutane lissafi.

Bayanin na Aminu Saira ya kuma haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin masu bibiyan shirin game da matsayinsa da kuma yiwuwar ci gaba da nuna wasan a tashar Arewa24.

Muhawarar mai zafi har a tsakanin manyan mutane da ba a zaton suna sha’awar fina-finan Hausa, saboda yanayin aikinsu ko matsayinsu shi ne wani abin mamaki.

Misali, likitoci mutane ne da ake ganin ba kasafai suke samun lokaci ba saboda yanayin aikinsu, balanta har su samu lokacin kallon fina-finai.

Amma Dokta Ibrahim Musa, Kwararren Likita a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) da ke Kano, na bibiyar fim din mai dogon zagno a tashar Arewa24, kuma bai ji dadin dakatar da nuna fim din da ka yi ba.

“Idan ban da shirmen Arewa24, ina aka taba [yin] haka? Kun hada fina-finai masu dogon zango manya (Kwana Casa’in da Labarina) da ke saka dattijai irina suna kallon tasharku suna nishadi, [amma] kun dakatar da su a lokaci guda.

“Na daina kalla sai kun dawo da su. Me ya sa ba za ku raba kafa ba, ku raba su ya zamanto idan daya yana karewa sai dayan ya tafi hutu. Idan ya dawo hutu, sai dayan ya huta,” kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Aminiya ta kuma gano cewa Dokta Ibrahim bai tsaya ga kallon fim din mai dogon zago ba, yakan kuma yi rubutun a kan wasan kwaikwayon daga lokaci zuwa lokaci.

‘Nakan bar sana’ata sabon fim din’

Nasiru mai nama, mahauci ne kuma magidanci da a kullum ba a rasa mutane masu da ke zuwa sayen nama a rumfarsa kuma, kuma ko yaushe ana kai-komo a wajen.

Amma hakan bai hana shi samun lokaci da yake sulalewa ya bar rumfar tasa don ya je ya kalli film din Labarina.

Ya shaida wa Aminiya cewa yakan bar shagon nasa ne ya je gida don su kalli shirin tare da iyalinsa cikin nishadi.

“Tare muke zama da iyalina mu kalla muna nishadi. Fim din ya yi kyau,” inji shi.

Mahaucin ya ce babban abin da ya sa ya fara kallon fim din mai dogon zango shi ne, “yadda na ji ana labarin shirin ne ya sa na fara bibiyan shirin’.

Nasiru ya ce duk ranar da ake nuna fim din, to da zarar lokaci ya kusa yake komawa gida, sai ya gama kallonsa tsaf sannan ya dawo ya ci gaba da sana’ar tasa.

“Nakan bar yara a wajen ne, in je in dawo. Ni kaina ina mamaki gaskiya,” inji shi.

Wani yanki da fim din Labarina

Shirin Labarina

Shirin Labarina, kamar yadda sunan ya nuna, wata budurwa ce, Sumayya (Nafisa Abdullahi) take ba da labarin rayuwarta da soyayyarta.

Fim din ya ta’allaka ne a kan jigon soyayya da amana da kuma sanin darajar soyayya.

Manyan masoyan su hada da Sumayya, da Mahmud wanda take tsananin nuna wa so da kauna mai tsafta.

Saboda tsananin son da take masa ta kori samarinta kamar su Presido da kuma Lukman, wadanda dukkanninsu masu kudi ne.

Shi ma Mahmud ya nuna wa Sumayya soyayya a zahiri, amma son bai kai wanda take masa ba, kuma yana nuna mata isa ne da kuma gadara.

A haka dai suka ci gaba da rayuwa har Mahmud ya hadu da Laila wadda saboda ita ya juya Sumayya baya ya nuna bai ma taba soyayya da ita ba saboda ya ga sabuwar budurwar tasa ’yar masu kudi ce.

Rabuwar Mahmud da Sumayya ya sa ta shiga tsananin tunani da damuwa cewa Mahmud din da take so ne zai yaudare ta, amma ta kasa yarda har sai da ta ji da kunnenta sannan ta gasgata hakan.

A kwana a tashi har ta cire soyayyar Mahmud a zuciyarta, ta fara mantawa da shi ta ci gaba da rayuwarta ita kadai.

Ana cikin haka ne Naziru Sarkin Waka ya saka ta a harkar waka har ta daukaka sosai a rayuwarta.

Ga shi kuma tana samun goyon baya daga mahaifiyarta da kuma kawarta Rukayya.

Abin da ya sa shirin farin jini

1. Tsarin shirin

Kasancewar mutane na sha’awan sauraren labarai ko dai na soyayya, ko na wasu abubuwan da daban, ya sa gidajen rediyo kan gabatar da shirye-shiryen karatun littafan labari, inda sau tari za ka ga mata sun taru suna sauraron shirye-hiryen.

A lokuta da dama idan dare ya yi, ko dai ka ga mata sun taru sun kunna rediyo daya, ko kuma kowacce ta koma gefe tana sauraro ko a waya ko a rediyo.

Shirya fim din a tsarin labari na daya daga cikin abubuwan da suka sa yake daukar hankalin mutane matuka.

2. Jigon soyayya da alamun cin amana

Jama’a, musamman Hausawa sun yarda da tsarin kowa ya ci nanin, dole nanin ta ci shi.

Yadda labarin ya taso an zalunci Sumayya, saboda haka masu kallo na so su ga yadda karshen Mahmud za ta kasance.

3. Aminu Saira

Aminu Saira, fitaccen darakta ne a masana’antar Kannywood, amma a kwanakin baya sai aka ji shi shiru.

Kwatsam kuma sai aka ji ya dawo a shirin Labarina.

Aminu Saira ya ba da umarni a fina-finai masu kyau, kuma ana masa ganin ba ya yin fim sai mai ma’ana.

Wannan mutuncin da mashiryin shirin ke da shi ya sa mutane son kallon fim din.

4. Talla
An tallata fim din ya sosai, musamman a kafafen sadarwa na zamani.

Jaruman Kannywood da dama suna tallata fim din a shafukansu na Instagram ko da kuwa ba sa ciki.