✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa kawalci wa ’yan bindiga ke neman zama sana’a

Masana sun ce talauci da rashin aiki da son zuciya ne ummul haba'isi

Yawan mutanen da ’yan sanda suka kama a kwanakin nan suna kai wa ’yan bindiga mata don su yi lalata da su alama ce ta yadda wannan abu ke neman zama sana’a ga wasu.

Wasu masana dai na ganin ba komai ne ya jawo hakan ba face rashin aikin yi da talauci.

A cewar Dokta Nuraddeen Usman Miko, wani masanin tattalin arziki a Jami’ar Jihar Kaduna, abubuwa da dama za su iya ingiza mutane kai wa ’yan dabar daji ’ya’yansu mata don su samu kudi, amma babu kamar wadannan dalilai biyu da kuma son zuciya.

“Ba karamin abu ba ne zai sa iyaye su kwashi yaransu su kai ma ’yan bindiga saboda kudi; ba abin da zai sa haka sai talauci”, inji shi.

Idan ba a manta ba, ’yan sanda a birnin Zaria na Jihar Kaduna sun baje kolin wasu mutane da suka kama suna safarar mata – matan aure da ’yan mata – zuwa Dajin Galadimawa, inda ’yan bindiga ke lalata da su.

A watan jiya ne dai Rundunar ’Yan Sanda ta IRT mai yaki da masu garkuwa da mutane ta kama masu safarar matan.

Dakan daka…

Daga cikin wadanda aka kama dai har da wata baiwar Allah, wadda ta shaida wa Aminiya cewa ta fi shekara guda tana kai wa ’yan bindiga ’yan mata, ciki har da ’ya’yan cikinta da na ‘yan uwa.

“Musamman, a yanzu da talauci ya yi yawa, wasu iyayen ba za su iya daukar nauyin ciyar da ’ya’yansu ba, sannan su kuma ’yan bindiga suna da kudi a hannunsu, za su iya ba [iyayen yaran] komai da suke bukata don su kansu su samu yadda suke so”, inji Dokta Miko.

Matar dai ta ce daya daga cikin ’yan bindigar, Dan Inna, dan uwanta ne; kuma shi ya kira ta ya ce ta yi mishi budurwa.

“Sai na ce mishi a yadda kuke, ka ga sana’arku ba mai kyau ba ce, yaya za a ce in ba ka lambar wata?”

Wannan, a cewarta, ya sa ta tambayi ’yar yarta wacce ta ke gidanta a lokacin ko tana son shi. Tun da yarinyar ta amsa tana son shi kuma sai aka ci gaba da soyayya.

Sai dai yarinyar ta ce ita ba ta taba kwanciya da wani daga cikin ’yan bindigar ba, ko da yake a wani lokaci da suka je dajin Dan Inna ya ba ta N6,000 sannan ya bai wa ’ya’yan gwaggon tata wacce ta hada ta da shi N2,000.

‘Ni ba kawali ba ne…’

Baya ga wannan mata, ’yan sandan na IRT sun kuma kama wani saurayi da wata budurwa wadanda su ma suke kai wa ’yan bindigar mata a Dajin na Galadimawa.

Saurayin, wanda ya ce shi ba kawali ba ne, ya ce gayyatar shi aka yi wata shida da suka wuce aka fada mishi cewa akwai wani aiki idan zai iya.

“Muka je wurin [wanda aka ce shi zai ba mu aikin] a Hayin Gada, hanyar Galadimawa; sai ya fada mana cewa yana so mu samo mishi ’yan mata haka…

“To da suka yi mana bayanin haka… sai muka amsa musu cewa za mu iya [saboda] in muka ce musu ba za mu iya ba za su iya harbe mu, ko su yi garkuwa da mu; muka ce za mu iya saboda mu samu mu rabu da su lafiya”, inji matashin.

Wannan saurayi ya tsaya kai da fata cewa daga shi har budurwar da ya gayyata ba su yarda sun shiga wannan harka ba; amma abin tambaya shi ne anya ba kwadayi ne ya sa suka amince tun farko su gana da wadanda za su ba su aikin ba?

A cewar Dokta Miko, “Idan talauci ya yi yawa komai na iya faruwa; mutane za su iya aikata komai don su samu kudi”.

Abin ya ki karewa

Masanin ya kuma ce kai wa ’yan dabar daji mata na cikin dalilan da ke tarnaki ga yakin da ake yi da masu garkuwa da mutane.

“Da ma hakan ne ya kara jefa wannan yakin namu cikin wannan halin da ake ciki.

“Ba shakka, hakan yana kara wa ’yan ta’adda karfin gwiwa domin ci gaba da aikata barnar da suke yi.

“Kuma hakan  zai sa su ma [masu] yi wa ’yan ta’addar safarar  mata su zama ’yan leken asiri a cikin al’umma”, inji shi.

Wannan ne ma ya sa, a cewar Dokta Miko, ya wajaba a samar wa matasa da sauran jama’a aikin yi.

“Baya ga matakan tsaro da gwamnati ke dauka, ya kamata kuma a kara samar da hanyoyin inganta rayuwar matasa, ta hanyar farfado da wutar lantarki don masana’antumu da suka durkushe su fara aiki.

“Su kuma gwamnatocin jihohi su koma gina madatsun ruwa domin karfafa norman rani – hakan zai samar wa [mutanen] karkara aikin yi, hakan zai rage shiga irin wannan muguwar sana’ar ta safarar mata suna kai ma ‘yan fashin daji”, inji Dokta Miko.

Matan aure

Daga cikin mutanen da aka kama ana zargin su da hannu a wannan harkar har ma da matan aure wadanda suke kai kansu a yi lalata da su a ba su kudi.

Daya daga cikinsu ta shaida wa Aminiya cewa tilasta mata wani mai garkuwa da mutane ya yi da barazanar za a sace ta da iyayenta.

“Ya ce in ban tsaya ya yi amfani da ni ba sai ya tafi da ni; na ce don Allah kar ya yi, ya ce sai ya yi…”

Bayan dan dabar ya biya bukata, inji ta, da farko ya ki ba ta ko da kudin mota, amma daga baya ya ba ta N5,000.

An sha samun rahotannin mutanen da ake zargi da kai wa ’yan bindiga kayan amfanin yau da kullum.

Su ma wadanda ake zargin suna safarar mata suna kai wa ’yan ta’addar wata hanya ce ta bude musu ta samun kudi.