✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa muka ba Amaechi sarauta — Sarkin Daura

Ban taba yin sarauta don kudi ko wani mukami ba.

A ranar Asabar ta makon da ya gabata ce Mai martaba Sarkin Daura, Dokta Umar Farouk Umar ya nada Ministan Sufuri Mista Rotimi Amaechi a matsayin Dan Amanar Daura.

Bikin nadin wanda ya samu halartar Gwamnan Jihar Kastina, Alhaji Aminu Bello Masari da wadansu manyan mutane da sarakunan da suka fito daga yankin da na Ministan.

Sarkin Daura ya ce sukan bayar da sarauta ce bisa cancanta, “Ban taba yin sarauta don kudi ko wani mukami ba.

“Duk wanda ya yi wa talakawan da aka ba mu amana aiki, za mu karrama shi a matsayin tukuicin abin da ya yi wa talakawanmu,” inji shi.

Ya ce “Allah Yana ganin zuciyarmu a kan abin da muke yi. Allah Shi ne alkalin kowa.”

Sarkin ya ce daga ko’ina mutum ya fito koda Bature ne, idan ya yi abin da ya cancanta ta hanyar kawo wa talakawansu abin ci gaba, masarauta za ta karrama shi ta hanyar ba shi wata sarauta.

A jawabin da Danejin Daura Alhaji Abdurrahaman Salihu ya karanta a madadin Masarautar Daura ya ce dalilan da masarautar ta nada Minista Amaechi a matsayin Dan Amanar Daura shi ne, “Samar da Jami’ar Sufuri a garin.

Fadada hanyar jirgin kasar da ta so daga Jihar Kano ta biyo ta Jihar Jigawa ta biyo garin Daura ta wuce zuwa Katsina har zuwa Maradi da ke Jamhuriyar Nijar.

Aikin zai shafi ci gaban rayuwar al’ummar wannan yanki musamman ta fuskar tattalin arziki da sauran makamantan haka musamman ta yadda aka ajiye babbar tashar jirgin a nan Jihar Katsina wadda tuni har an kai wadanda za su yi wannan aiki wajen kuma an kaddamar.”

Danejin, har ila yau ya ce, masarautar ta sake duban wani dan kasuwa mai suna Alhaji Nasiru Haladu Dano wanda ta ce, mutum ne wanda ya tallafa kuma ya bayar da gudunmawa wajen ganin matasa ba sa zaman banza, wanda al’ummar masarautar shaida ne a kan haka.

Shi ma masarautar ta karrama shi da Sarautar Tafida Babba na Daura.

Aminiya ta ruwaito cewa, an yi bikin nadin wadannan sarautu biyu a garin na Daura, a cikin kwanciyar hankali da annashuwa.