✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Abin da ya sa muka kashe Ahmed Gulak’

Barazanar rasa raina ce ta sa na amince da bukatar wadanda suka harbi Ahmed Gulak.

Rundunar ‘yan sandan Jihar Imo ta sanar da kama daya daga cikin wadanda ake zargi da kashe jigo a jam’iyyar APC, Ahmed Gulak.

An ranar 30 ga watan Mayun 2021 ne wasu ’yan bindiga suka harbe Ahmed Gulak a birnin Owerri na Jihar Imo yana shirin komawa Abuja.

Da yake zantawa da manema labarai a ranar Litinin, mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Imo, Mista Mike Abattam, ya ce mutumin da ake zargi mai suna Anosike Chimobi wanda dan asalin Karamar Hukumar Ahiazu Mbaise ne yanzu haka yana hannu kuma ana ci gaba da bincike a kansa.

Da yake gabatar da wanda ake zargin tare da wasu, mai magana da yawun ’yan sandan ya ce Chimobi ya kasance daya daga cikin mutanen da suke nema ruwa a jallo tun bayan kashe Gulak a bara.

Ya ce wanda ake zargin ya tsere ne a yayin wani artabu tsakanin jami’an ‘yan sanda da ‘yan kungiyarsa a Aboh Mbaise, jim kadan bayan kisan Gulak, inda aka kashe biyar daga cikin wadanda ake zargin.

A nasa bayanin ga manema labarai, Chimobi ya ce shi dai ya kasance direban motar haya kuma ba shi da wata alaka da wani gungun masu aikata laifi a jihar.

Sai dai Chimobi ya ce wadanda suka kashe Gulak sun nemi ya dauke su a motarsa zuwa wurin da lamarin ya faru, amma bayan ya yi yunkurin yin tirjiya, sai suka yi barazanar kashe shi, lamarin da ya sanya ya amince da bukatarsu.

Ya ce shi ne ya kai ababen zargin har wurin kuma ya tare motar da Gulak din ke ciki a yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa filin tashi da saukar jirage.

Da yake bayani dangane da yadda aka kashe  Gulak, Chimobi ya ce mutanen da ya dauko a motarsa sun harbe shi ne bayan ya ki sauka daga motar da yake ciki kamar yadda suka bukata.

Ya ce bayan faruwar haka ne sai suka tsere wanda a kokarin kuma suka ci karo da jami’an tsaro, inda aka bude musu wuta.

Marigayi Ahmed Gulak wanda hadimi ne ga tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan kan harkokin siyasa, wasu ’yan bindiga sun harbe shi yayin da ya kai ziyara Jihar Imo.

Aminiya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne bayan da ‘yan bindigar suka kai hari kan wata motar tasi kirar Toyota Camry dauke da Ahmed Gulak tare da wadansu mutum biyu da ke kan hanyarsu ta zuwa tashar jiragen sama.