✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa muka sayi Mikel Obi —Stoke City

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Stoke City ta Ingila, Michael O’Neil ya ce sai da suka yi bincike, suka gano cewa Mikel Obi zai taimaka…

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Stoke City ta Ingila, Michael O’Neil ya ce sai da suka yi bincike, suka gano cewa Mikel Obi zai taimaka musu matuka kafin suka dauko shi.—

Tshon kyaftin din Najeriya, Mikel Obi ya amince da kwantiragin shekara daya ne da kungiyar, wadda ke rukuni na biyu na Firimiyar Ingila a ranar Litinin da ta gabata bayan ya raba gari da kungiyar Trabzonspor a watan Maris na bana.

Mikel Obi ya yi fice ne a zamanin da yake kungiyar Chelsea ta Ingila, inda ya yi shekara 11, kafin daga bisani ya koma kungiyar Tianjin Teda a China a shekarar 2017.

Daga can ya sake dawowa kungiyar Middlesborough ta Ingila a shekarar 2019.

“Mun yi tunanin dauko shi ba zai yiwu ba, amma bayan binciken da muka yi, sannan kuma bayanan da ya yi kwana daya, ya nuna jin dadinsa kan shirye-shiryenmu, muka kuma amince da yanayin tunaninsa, sai muka samu matsaya.

“Dan wasa irin Mikel wanda ya buga manyan kungiyoyi, ba za ka samu damuwa ba sosai idan ya zo wajenka a rukuni na biyu.

“Amma duk da haka sai da muka tambayi mutanen da ya yi aiki da su a baya irinsu Tony Pulis da sauransu.

“Muhimmin dai shi ne shi Mikel din ya nuna sha’awarsa na zuwa, sannan kuma mun ga amfanin da zai yi mana.”