✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abin da ya sa muka takaita tattakinmu a Suleja – ’Yan Shi’a

Kungiyar ta ce ta dauki matakin ne don kauce wa shiga hjhakkin jama'a.

Mambobin kungiyar mabiya Shi’a ta Najeriya (IMN) sun ce a bana sun takaita tattakinsu mai taken ‘Arba’una’ a garin Suleja na Jihar Neja ne don gujewa shiga hakkin jama’a da cunkoson ababen hawa.

Dubun-dubatan mabiyan Sheikh Ibrahim El- Zakzaky da su ka hada da mata da kananan yara ne suka bi ta wasu manyan titunan garin a ranar Litinin, su na wakokin tinawa da zagayowar ranar kisan gilla ga Imam Hussain, jikan Manzon Allah (S.A.W.).

Wani jagoran kungiyar, malam Aliyu Tirmizi wanda ya zanta da Aminiya a kan lamarin, ya ce sun gujewa bin manyan tituna irin na Abuja zuwa Kaduna ne sabanin yadda su ka saba a baya, don magance mummunar cunkushewar ababan hawa a muhimmiyar hanyar.

Aminiya ta ba da labarin yadda irin hakan ya kai ga rasa mambobin kungiyar shida a shekarar 2018, biyo bayan arangamarsu da wanin ayarin soja da ke jigilar makamai zuwa Kaduna, da su ka ratsa ta inda su ke tattakin, a kan babbar hanyar Zuba da ke Abuja.

Saindai tattakin na ranar Litinin da ya faro daga kauyen Maje da ke wajen garin Suleja sannan ya karkare a tsakiyan garin, shi ma ya jawo cunkushewar hanya tare da tilasta wa masu ababen hawa sauya hanya.

Kazalika, wadanda ya ritsa da su kuma su ka hakura har zuwa lokacin da su ka samu damar sauya hanya.

A cewar Malam Aliyu Tirmizi, mambobinsu daga Jihohin Arewa ta tsakiya da kuma yankin Kudancin kasar nan, wadanda dukkansu ke karkashin shiyyar Kaduna, sun halarci tattakin.

Da a ka tuntube shi, babban kwamandan ’yan sanda na shiyyar Suleja, ACP Sani Badarawa, ya ce ba a fuskanci wata matsalar hayaniya ko rauni ba a yayin tattakin wanda ya karkare da bayanai daga wasu fitattun ’yan kungiyar.