Daily Trust Aminiya - Abin da ya sa muke adawa da sulhu da ’yan bindiga – Shehu Al
Subscribe

A hagu, Shehu Aljan ne a Kano, yayin da ‘yan sanda suka gabatar da wani da ake tuhuma gaban manema labarai

Abin da ya sa muke adawa da sulhu da ’yan bindiga – Shehu Aljan

Wani fitaccen mai kama barayin shanu da masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata miyagun ayyuka a kasar nan, Alhaji Shehu Musa da aka fi sani da Shehu Aljan ya nuna rashin goyon bayansa ga sulhun da wadansu gwamnoni ke yi da ’yan bindiga a yankunan Arewa.

Shehu Aljan ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da Aminiya a Abuja, inda ya ce abin mamaki ne yadda aka mayar da mutanen Arewa tamkar wasu raguna, inda za a sace mutum sai an biya kudi kafin a dawo da shi. Kuma kudi mai yawa ba kadan ba.

“Kudin fansar da ake bayarwa idan an sace mutum shi ke dada jawo harkar garkuwa da mutane ke kara tasiri, amma idan za su sace a kyale su, dole su sako mutum idan har kwanansa ba kare ba,” inji shi.

Shehu Aljan ya ce gwamnoni su daina yin sulhu da ’yan ta’adda domin yin hakan kuskure ne, a bari su da jami’an tsaro su yi maganinsu. “Game da batun sulhu da wadansu gwamnoni ke yi da ’yan ta’adda, musamman masu garkuwa da mutane, ba na goyon bayan haka. Domin sau da dama idan aka yi sulhun, makaman da tubabbun ’yan bindigar suke kawowa ba su taka kara sun karya ba.

“A lokacin da barayin suke kawo farmaki garuruwan mutane, za ka gan su kamar mutum 100 zuwa sama a kan babura kuma kowannensu dauke da bindiga. Amma da zarar an ce an yi sulhu, sai ka ga sun kawo bindigogi uku ko biyar. To sauran makaman ina suke? Ka ga ke nan da sauran rina a kaba,” inji Shehu Aljan.

Aljan ya kuma yi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari akwai bukatar ya zauna da gwamnonin da suke cewa za su sulhunta da ’yan ta’adda, domin a fahimtarsa idan har za a rika zaman sulhu da barayin, me zai sa kuma ana narkar da kudi da sunan tsaro? Saboda duk Gwamnan da zai yi sulhu da ’yan ta’adda babu maganar a ce ana ware wasu kudade na musamman da sunan samar da tsaro, tunda ba barayin ake bai wa kudin ba.

Ya ce a matsayinsa na Shugaban Sashen tsaro na Kungiyar Miyetti Allah, ba za su zuba ido tsaro ya tabarbare a kasar nan, ba tare da sun bayar da gudummawarsu wajen ganin an samu ingantaccen tsaro a Najeriya ba.

“Idan ka duba a cikin kwana hudu mun yi nasarar kama barayin shanu a Kano. Ka ga idan sauran gwamnonin Arewa da suke fama da matsalar ’yan ta’adda za su bayar da hadin kai kamar yadda Gwamnan Kano Dokta  Ganduje ya bayar, da tuni an toshe barakar da ake samu a fannin tsaro. Don haka ina kira ga gwamnonin su yi koyi da Gwamna Ganduje wajen yakar ta’addanci domin tabbatar da tsaro a jiharsu. Shi ya hada kai da jami’an tsaro wadanda suka hada da ’yan sanda da sojoji da ’yan sa-kai, inda ake aiki ba dare, ba rana a birni da kauyukan Jihar Kano,” inji shi

Ya kuma ce tsakaninsa da jami’an tsaron da suke fita aiki akwai kyakkyawar fahimta, domin suna ba shi hadin kai yadda ya kamata.

Ya ce ya haura shekara 20 yana harkar kama barayi, kuma ya samu nasarori da dama, inda ya kama barayi a jihohin Kogi da Neja da Taraba da Katsina da Nasarawa da Filato da Bauchi da sauransu. Kuma yanzu yana bakin aiki a Jihar Kano kuma ya sha alwashin ganin bayan barayin shanu da masu garkuwa da mutane da sauran ’yan ta’addan da ke jihar.

More Stories