✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa na cire dana daga makarantar gwamnati – El-Rufa’i

Gwamnan ya ce sau bitu makarantar na fuskantar barazanar kai hari daga 'yan bindiga.

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya bayyana dalilin da ya sa ya cire dansa, Abubakar Sadik El-rufa’i, daga makarantar gwamnati ta Kaduna Capital a sirrance.

A shekarar 2019 ce dai Gwamnan ya kai dan nasa makarantar wacce da yace daga cikin wadanda suka fi dadewa a Arewacin Najeriya.

To sai dai Aminiya ta rawaito yadda Gwamnan ya cire Sadik din a sirrance ba tare da sanar da kowa ba.

Babban Mai Taimakawa Gwamnan kan Harkokin Watsa Labarai, Muyiwa Adekeye ` ki cewa uffan lokacin da wakilinmu ya bukaci jin ta bakinsa a kan lamarin.

To sai dai a wata tattaunawa da sashen Pidgin na BBC, El-Rufa’i ya ce ya cire shi ne saboda barazanar da ’yan bindiga suke yi masa, la’akari da matsayin da ya dauka na kin biyan diyya gare su.

Gwamna Nasir El-Rufa’i da mai dakinsa, Hajiya Ummi El-rufa’i lokacin da suka kai dan nasu makarantar.

‘’Ya’yana biyu ne a makarantar’

Gwamnan, wanda ya ce wannan ne karo na farko da zai yi magana a kan lamarin ya kuma ce ban da Sadik din ma, akwai wata ’yarsa mai suna Nesrin da ita ma ya saka ta a makarantar ta gwamnati lokacin da ta kai shekara shida.

Ya ce ko da yake babu wata barazana ta zahiri ga Nesrin, an bashi shawara ne ya cire su saboda dalilai na tsaro.

“Na yi wa ’ya’yana rijista a makarantar, amma dole tasa muka janye su na dan wani lokaci saboda dalilai na tsaro.

“Akwai rahotanni da muka samu har sau biyu na masu yunkurin kai wa makarantar hari saboda su dauke su.

 “Amma bana tunanin zasu sami nasara saboda irin tsaron da zamu samar, kawai dai bama so mu jefa rayuwar ragowar yaran makarantar cikin hatsari.

“Bamu san irin makaman da zasu zo da su ba. Na riga na dauki matsayi kan kin biyan kudin fansa ga ’yan bindiga, kuma mun kama akalla rukuni uku na ’yan bindiga da suke shirin kai hari don su sace dana su ga ko zan biya fansar ko a’a,” inji Gwamnan.

Ya tsaya kai da fata cewa ya dauki matakin ne saboda lafiyar sauran yaran, inda ya ce ya saka shi a makarantar ne tun da farko domin ya nuna wa al’ummar Jihar irin kwarin gwiwar da yake da shi kan makarantun gwamnati.

Ya kara da cewa har yanzu Sadik yana nan a matsayin dan makarantar kuma yana zuwa ya yi jarrabawa, kawi dai yanzu a gida yake karatu, har zuwa lokacin da zai tabbatar babu sauran barazanar tsaro kafin su koma,” inji shi.

‘In na kammala mulki za mu bar Kaduna’

El-Rufa’i ya ce, “Burina shine za su ci gaba da zama a makarantar har na sauka daga mulki, saboda in na kammala wa’adina zan bar Jihar ne, daga nan zan yanke shawarar canza musu wasu makarantun.”

Gwamnan ya ce dan nasa yana kewar makarantar matuka kasancewar ya kan tambaye shi, “Baba, yaushe zan koma makaranta? Ina kewar abokaina da malamaina, amma na ce masa ba yanzu ba, za a iya sace ka,” inji El-rufa’i.

A ranar Asabar dai Aminiya ta rawaito muku yadda Gwamnan ya cire Sadik daga makarantar, sabanin yadda mutane suka rika zaton matakin zai taimaka wajen inganta ilimi a Jihar.

Mazauna yankin da makarantar take sun nuna takaicinsu kan yadda gwamnan ya cire dan nasa, watanni kadan bayan ya fara cudanya da sauran ’ya’yan talakawa a inuwa daya.

Mutane da dama dai a lokacin sun dauka sanya Sadik a makarantar gwamnatin a matsayin matakin da zai inganta harkar ilimi a Jihar.