✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa na dade ana damawa da ni a Kannywood —Aminu Saira

Aminiya ta zanta da fitaccen darakta a masana’antar Kannywood, Malam Aminu Saira, inda ya tabo batun yadda ya fara ba da umarni, fim dinsa mai…

Aminiya ta zanta da fitaccen darakta a masana’antar Kannywood, Malam Aminu Saira, inda ya tabo batun yadda ya fara ba da umarni, fim dinsa mai dogon zango, Labarina da sauransu.

A kwanakin baya ka sanar da za a je hutun haska fim din Labarina, inda wasu suke cewa kun samu matsala ne da Arewa24?

Babu wani sabani tsakaninmu da Arewa24, kawai dai mun gama zango na 1 da 2, wanda su ne muka yi yarjejeniya da su.

Yanzu za mu je zango na 3 da 4, to sai mun gama, sannan mu zauna da su, idan mun cin ma wata yarjejeniyar, sannan idan zai ci gaba a wajensu, sai a ci gaba.

Wannan ne kawai ba wai wata sabani ba ne.

Mutane suna ta tsammani da shaukin jiran ci gaban shirin. Wane albishir za ka musu?

Muna bakin kokarinmu, amma gaskiya muna ta kokarin ganin cewa ya fi na baya samun ingantuwa ta kowane vangare, kamar bangaren labari da kayan aiki da duk wasu abubuwan da za su taimaka wa shirin.

Sannan duk wasu kura-kurai da muka gani, ko mutane suka ankarar da mu, to in sha Allah muna kokarin ganin kauce wa wadannan abubuwan.

Amma ina da yakinin da yardar Allah zango masu zuwa za su fi wadanda aka kalla.

Manyan mutanen Arewa da sauransu da a da babu ruwansu da Kannywood, suna ta maganar Labarina yanzu, me kuka yi daban da ya jawo hankalinsu kuma yaya kake ji?

Wallahi ya ban kwarin gwiwa sosai, kuma na gode wa Allah matuka da hakan ya faru.

Sannan wannan sai ya kara ba mu kwarin gwiwa cewa mutanenmu suna biye da mu, kuma suna sane da abin da muke yi.

Watakila da din da ba sa magana bai kai inda ya kamata ba ne, ko kuma bai gamsar da su ba.

Amma yanzu watakila abin da muke yi a Labarina ya gamsar da su, sai suke magana.

Sannan sai kuma ya kara min wani tunanin cewa wannan kafar tamu mu kara rike ta da muhimmanci kuma a rika kokarin fito da wasu  sakonni ba iya matasa ba kawai, har da manyan tunda ga shi wannan ya shiga zuciyar kowa.

Amma wallahi na yi murna matuka sannan ina yaba musu tare da godiya bisa lokacin da suke ba mu na kallon wanna shirin.

Na yi magana da farfesoshi da suka kalla, idan sun ga wani abu kuma suna min magana, idan ba su fahimta ba ne, mu musu bayani, idan kuma kuskure ne, sai mu karva mu gyara, amma abin farin cikin shi ne,
yabon ya fi gyaran yawa.

Me ya sa kuka zabi nuna shirin a Arewa24 maimakon a YouTube da ake tunanin za ku fi samun kudi?

Da farko mun yi tunanin a sa a CD ko talabijin, to kuma sai ya kasance kasuwar CD ta mutu.

Arewa24 kuma sun nemi mu yi kasuwanci da su, da muka zauna da su, muka yi yarjejeniya sannan muka ga mun gamsu sai muka amince.

Sannan suka ce suna da manhajar ‘Arewa on Demand’, wanda za ka iya kallon shirin a duk inda kake a fadin duniya, sai suka bukaci a hada da shi a cikin yarjejeniyar.

Sai kuma muka ga alfanun Arewa24 din ya fi, dalili kuwa shi ne ko
da mu za mu samu kudi fiye a YouTube, amma idan muka duba yadda shirin zai zagaya a lokaci daya, saboda Arewa24 lokaci daya za a haska shi.

To duk ranar da za a nuna, miliyoyin mutane za su zauna su kalla, to na kalla kowa ya kallo sai dai wanda zai yi maimaici ko kuma ka kalla a manhajar, savanin a YouTube, wanda wani ya kalla yau, wani gobe da sauransu.

Wadannan da sauransu muka lura, sannan muka lura zai fi sauki ga mutane a Arewa24.

Don haka akwai nema wa masu kallo sauki da sauran dalilan da muka duba duk da cewa wasu sun fi son YouTube din.

Amma tunda za a sa talabijin, sannan a sa a manhajarsu din da za a iya kallo a duk fadin duniya, sannan bangaren da idan aka juya tashar Arewa24 din takan zo a kyauta wato ‘free to air’, sannan ana kallon Arewa24 a duk Afrika sai muka ga ya fi.

Ke nan kun lura da saukaka wa mutane sama da riba, kasancewar ana tunanin za ku fi samun riba a YouTube?

Na yi tunanin hakan gaskiya, amma na yi tunanin kowa ya kalla a lokacin da ya kamata a kalla.

Yanzu idan muka ce a YouTube za mu sa, wani yana kauye ba shi da yanar gizo, ba zai samu kallo ba.

Kuma muna da dimbin masoya, to gara a kai inda ko da ba za mu samu ribar ba za ta kai ta can din ba amma zai fi sauki ga masu kallonmu masoya.

Zuwa yaushe za a tsimayi ci gaban shirin?

Nan ba da jimawa ba za mu sanar da ranar da za a cigaba da kallon shirin.

Dama tsarin shi ne ba za mu sanar ba sai mun yi aiki da yawan da idan muka fara nunawa za a dade ana haskawa.

Mutane da yawa suna cewa saboda Aminu Saira ne suke kallon shirin, ko akwai wani abu da kake yi ne na daban?

Ni dai kullum ina cewa abu uku nake rikewa:

Na farko shi ne mutuncina, wato ya zama komai nake yi yana da tsafta babu Allah wadai.

Na biyu juriya, ya zama komai za ka yi ka jure saboda dole za ka hadu da abubuwa iri-iri, sai ka jure har ka cimma burinka.

Na uku shi ne, kullum ina kallon da a ce Allah wadai, gara a ce ban yi ba, shi ya sa kusan shekaru ina zaune, mutane sun yi, sun yi, to kuma idan ka yi, CD din babu kasuwa, kuma ’yan kallo da me za su kalle ka.

To ina ganin wadannan abubuwan su ne sirrin, amma ban sani ko  watakila akwai wata kudura daga Allah ba, amma na fi tunanin wadannan abubuwan ne.

A cikin fina-finanka, wanne ne ka fi so?

Akwai bambanci tsakanin daukaka da so. Idan ka ce wanda na fi so, zan ce ‘Ga Duhu Ga Haske.’

Amma duk fim dina, ina son su, amma kuma idan maganar daukaka ake yi, yanzu Labarina ake magana.

Ba ma a san ina maganar Labarin zai tsaya ba, kuma irin tafiyar da yake yi, sai yake nuna kamar zai shafe tarihin sauran fina-finanmu.

Ni ma ina son Labarina sosai, son ne ma ya sa muka bata lokaci, na kashe kudi sosai domin a inganta shi.

Amma gaskiya na fi son Ga Duhu ga Haske saboda wasu sakonni da fim din ya kunsa da kuma wani alfanu da muka samu a lokacin.

Akwai kuma mutanen da suka min magana cewa akwai wata mata da za ta Musulunta a Katsina, inda ta ce tana son suna Zainab, sannan ta ce za ta Musulunta ne saboda wani fim da ta kalla Ga Guhu Ga Haske.

Haka a Gombe an samu irin wannan labarin.

Mece ce babbar nasarar da ka samu a fim?

Ita ce na gode wa Allah da yau shekara goma sha, wasu sun biyo ni tun fim dina na farko Musnadi, har yanzu.

To ka ga babbar nasarar ita ce ka shekara da shekaru da wannan mutuncin kuma har yanzu ba a cewa kaico, kullum yabo ake yi.

Duk abin da na samu na daukaka da sanin manyan mutane, wallahi ba  su kai min samun masoya da suke bi na suka yarda da ni kuma muke tafiya tare na tsawon lokaci ba.

Wannan shi ne babban farin ciki kuma shi ne babban nasara, kuma ina fata har mu bar duniya a ci gaba a haka.

Yaya aka yi ka shiga masana’antar Kannywood?

To ni dai kawai kamar manufa ce.

Wani fim muke kallo na Amurka ni da wani abokina Mahmud, sai na ga kamar akwai sabo a ciki, sai na ga kamar ana sukar Musulunci, to kawai sai na ce masa ya kamata mu fara rubuta labari, mu shiga masana’antar muna shirya fina-finai mu rika mayar da martani a kan irin wadannan fina-finan to ka ji dalili.

Sai muka hadu da mu da Auwalu Sabo, Shugaban Kamfanin Sarauniya; A haka muka saba da shi.

Sai na tambaye shi mene ne ruhin fim, sai ya ce min labari da shiryawa da ba da umarni; da na yi bincike, sai na ga ra’ayina ya karkata a ba da umarni; Sai na ce nan ya kamata in rike.

To a haka na ci gaba, ina makaranta.

Da farko muna ta magana da mahaifina, ya damu kamar zan bar
makaranta, sai na ce masa ba zan bar karatu ba.

To a haka muka fara ina taimaka wa Aminu Sabo a matsayin mataimaki, daga nan Allah Ya sa muka samu tsaya muka da kafarmu, Na bude kamfanina Saira Movies, na fara fim da Musnadi.

To ka ji yadda gwagwarmayar ta faro har Allah Ya kawo mu yanzu.

Wane kira kake da shi zuwa ga masoya?

Su yi hakuri da mu. Kuma muna tunanin babu wata tashar da za mu haska shirin sama da Arewa din idan ba wani akasi aka samu ba.

Idan kuma Allah Ya daidata mu, a nan za a ci gaba. Muna godiya gare su.