✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa na fice daga PDP —Abba Gida-gida

Mun amsa kiran al’umma muka bar jam’iyyar zalunci.

A ranar Lahadin da ta gabata ce tsohon dan takarar gwamnan Jihar Kano a zaben 2019, Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa NNPP.

Wannan na zuwa ne bayan wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudanar a ranar Lahadin a mazabarsa ta Diso da ke Karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano.

Da yake bayyana dalilin ficewarsa daga jam’iyyar PDP, Abba Kabir ya ce “Ba za mu ci gaba da jure zaluncin da jam’iyyar PDP take manta ba, sun jima suna wulaƙanta jagoran Kwankwasiyya, duk da halaccin da ya yi musu.

“A wannan filin muka hadu a shekarar 2018 muka ce mun fice daga APC, saboda zaluncin da ake yi wa talakawa, muka koma PDP da sa ran abubuwa za su sauya” a cewarsa.

Ya ci gaba da cewa “Mun dauka PDP za ta dauki darasi ta nuna wa al’ummar Kano da suka fito suka zabeta a 2019 kauna, amma sam sai wulakanci da zalunci.

“Mun yi zaton akwai banbanci tsakanin APC da PDP, mun dauka za a samu adalci da bunkasar tattalin arziki, za a tallafa wa mata da inganta harkokin ilimi, amma sam ba a nan manufarsu take ba.

Abban ya kara da cewa “Mun gano ’yan jari hujja ne, an dade ana zaluntarmu ana wulakanta jagoran Kwankwasiyya, yanzu lokaci ya yi da masoya Kwankwaso suke kira gareshi, garemu da mu bar zama a cikin wannan azzalumai.

“An yi nazari an tabbatar da cewa abin da jama’ar Kano suke so shi ne abin da za mu runguma, saboda haka bayan nazari mun yarda cewa wannan jam’iyya ta NNPP ita ce wadda za ta taimaki talakawa”.

“Duk inda alheri ya ke a nan muke, duk inda amana take a nan muke, ba ma cikin azzalumai, ba za mu zauna a cikinsu ba, duk wanda baya son ci gaban al’umma muma bama son shi har a bada.

“Wannan shi ne babban dalilin da ya sanya muka yi shawara muka amsa kiran al’umma muka bar jam’iyyar zalunci” a cewar Abba Gida-gida.

Gidan Rediyon Freedom ya ruwaito Abban yana kakkausar suka ga ’yan jam’iyyar PDP inda ya kira su da kalmar munafukai, ya kuma yi tir da PDP kan fifita wadanda ya ce sun shiga gwamnatin APC an basu mukamai ta bayan fage a kansu.