✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa na tube Sanusi daga Sarautar Kano —Ganduje

“Da na zama Gwamna, sai na ce za yi maganinshi yadda yadda Jonathan ya yi masa a CBN."

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana dalilin da ya sa ya cire Muhammadu Sanusi II daga sarautar Kano.

Gwamnan ya ce ya dauki matakin a wancan lokacin ne domin ceto sarautar garagajiya daga wulakantawar da tsohon sarkin ya tashi yi mata.

Ganduje na wannan bayanin ne a Abuja ranar Litinin yayin bikin kaddamar da wani littafi a kan tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan wanda wani dan jarida, Bonaventure Philips Melah ya wallafa.

Ya ce tun farko ma ba Sanusin ne ya fi cancanta da sarautar Kanon ba lokacin da aka nada shi a watan Yunin 2014, yana mai cewa an nada shi ne kawai domin a bakanta wa tsohon Shugaba Jonathan.

A watan Afrilun 2014 ne Jonathan ya dakatar da Sanusin daga matsayinsa na Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) bisa zargin da ya yi wa wasu kusoshin gwamnatin tsohon shugaban na sace kudaden da yawansu ya kai Dala biliyan 49 daga lalitar gwamnati.

Ganduje ya ce kamata ya yi tsohon Gwamnan Bankin ya tattauna batun cikin sirri da Jonathan din wanda shi kuma zai iya ba da umarnin yin bincike ba tare da yayata wa duniya ba.

A cewar sa, “Jonathan ya dauki matakin da ya dace na korar Sanusi duk da lamarin ya janyo masa bakin jini a wancan lokacin.”

Kasa da wata biyu da cire shi daga Gwamnan Bankin, Sanusi ya dare karagar Sarkin Kano, matsayin da Ganduje ya ce ba cancanta ce ta kai shi ba.

A ranar 9 ga watan Maris, 2020 ne Ganduje ya tube Sanusi daga sarautar Kanon.

“Lokacin da na zama Gwamnan Kano, na ce hakika irin yadda Jonathan ya yi maganin Sanusi haka ya kamata nima na yi.

“Irin wannan maganin, duk da yake ni ba likita ba ne zai yi maganin cuta iri daya a kan mara lafiya daya.

“A kan haka ne na dauki wannan matakin domin na ceto sarautunmu daga durkushewa, kuma na yi abin da ya kamata.

“Saboda haka da ni da Jonathan mun dauki mataki iri daya. Ba na da-na-sanin abin da na aikata ko kadan,” inji Ganduje.