✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa yaki da ’yan bindiga yake da wahala – Gwamnati

Ministan ya ce gwamnati mai ci na iyakar kokarinta wajen magance kalubalen tsaro

Gwamnatin Tarayya ta ce yaki da ’yan bindiga a Najeriya yana ba da matukar wahala ne saboda salon da suke amfani da shi wajen aikace-aikacensu.

Ministan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakan, lokacin da ake tattaunawa da shi a cikin wani shiri a gidan rediyon Bond FM a karshen mako.

Ya kuma ce gwamnati mai ci na iyakar kokarinta wajen magance kalubalen tsaro a kasar, inda ya ce za a gani a kasa ne kawai idan ’yan kasa suka mara wa gwamnati baya.

Da yake tsokaci kan kalaman Gwamnan Kaduna, Nasir El-ufa’i kan shigo da sojojin haya daga waje muddin gwamnati ta gaza kawo karshen kashe-kashen, Ministan ya ce, “Gwamna El-rufa’i ya yi magana ne cikin damuwa a kan matsalar.

“Watakila yana magana ne duba da yadda ’yan bindigar ke cin karensu ba babba ba tare da shayin kowa ba.

“Ba za a taba kamanta sojojin hayar da namu na gida ba; yaki da ’yan bindga na da matukar wahala saboda yanayin da suke ayyukansu.

“Ba zai yiwu mu tare karfinmu waje daya mu je mu far musu ba, sai mu je muna kashe mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, ba ma son haka ta faru.

“Idan muka ce za mu debo sojojin haya daga waje, dole mu kwan da sanin cewa ba namu ba ne, kuma komai daren dadewa wata rana za su koma inda suka fito bayan kammala aikinsu,” inji Lai Mohammed.

Ministan ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su hada hannu da Gwamnatin Tarayya wajen yakin, inda ya ce gwamnatin ba za ta iya yi ita kadai ba.