✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ’yan Najeriya ke cewa kan Harin NDA

’Yan Najeriya sun ce an ji kunya, dole a tashi a yi abin da ya dace.

’Yan Najeriya sun ce abin kunya ne harin da ’yan bindiga suka kai Kwalejin Horas da Kananan Hafsoshin Sojin Najeriya (NDA), inda suka kashe manyan hafsoshi biyu, suka kuma sace wani.

Bayan tabbatar da faruwar harin da Hukumar Gudanarwar NDA ta yi a safiyar Talata, ’yan Najeriya a kafafen sa da zumunta sun ce harin ya nuna raunin tsaro a kwalejin, wanda kuma ke bukatar mahukunta su tashi su yi abin da ya kamata.

Wasu daga cikinsu kuma na ganin harin da aka kai wa kwalejin sojin ya nuna rashin tsaro a Najeriya ya kai makura, babu wanda ya tsira daga harin ’yan bindiga.

A sharhinta, Mariya Umar Dan Yaya ta ce, “Wannan al’amari yana da ban mamaki tunda har aka sace Manjo, kowa ya yi ta kanshi kuma wallahi abin kunya ga sojoji.”

“Lallai abin ya kai intaha a kasar nan, wato sun gane sojin Najeriya duk hotiho ne, za su kai hari har cikin gidansu, su kuma yi garkuwa da manyansu,” inji Muhammad Al-Shamrani.

– Sai ta-kai-ta-kai

Da yake tsokaci a kan lamarin, Abuh Bah Khar ya ce, “Abun nan babba ne, wanda kake tunanin zai kare ka yau shi ne ake sacewa.”

Musa Auwal ya ce, “Idan har za a kai wa NDA hari, to babu wanda ya tsira. Sai dai kawai mu yawaita yi wa kasar nan addu’a.”

Mahmud Ibrahim Abdul’aziz, ya ce, “Abin fa ya yi yawa fa, NDA fa aka shiga, ina kuma ga kauyuka? Allah dai Ya kyauta ya ba mu wanda ya fi Manjo alheri.”

Sharu Babangida, “Wannan abin kunya da me ya yi kama? Mu ma sai mu yi ta kanmu tunda hukumar da ke da alhakin kare ’yan kasa ta fada tarko.”

Abd Ler Thev, ya ce, “Idan har ’yan bindiga za su kai wa barikin soji hari, to gaskiya kasar nan babu tsaro.

“Zan iya fada da babbar murya cewa Rundunar Soji ba ita ke da alhakin kare raina da dukiyata ta kamar yadda take fada.”

Abdulkarim D. Umar ya ce, “Tofa su kansu sojoji ba su tsira ba, ina ga talaka irina, irinka. Allah dai Ya kawo mana karshen wannan matsalar da ta addabi kasarmu Najeriya.”

Nazifi Isyaku ya ce, “Kai! Dan Allah ina da tambaya wai wannan labarin daidai yake kuwa ko kuwa ni ne ba daidai ba, ina mafarki ne? AI kuwa in dai ba ba mafarki nake ba, to kuwa lallai ’yan kasata muna cikin tashin hankali. Shawara daya ita ce mu kara yawaita Istigifari gaskiya.”

Amma Sani Salhu Dauda ya ce, “Watakila wannan ya sa su tashi su yi abin da ya dace a kan ’yan bindiga, ko su bar kasar a hannunsu.”

– Yadda aka kai Harin NDA

Da tsakar dare, kafin wayewar garin Talata ne ’yan bindiga suka kai Harin NDA suka yi garkuwa da wani hafsan sojin kasa, Manjo Datong, sannan suka yi garkuwa da wani hafsan sojin kasa mai mukamin Sakan Laftana, Onah, wanda a halin yanzu yake samun kulawa a asibitin kwalejin.

Kakakin NDA, Manjo Bashir Jarira ya ta tabbatar da faruwar lamarin, wanda ’yan Najeriya ke cike da mamakin harin na harin na ranar Talata da ’yan bindiga suka harbi wani hafsan soji, a kwalejin mai tsauraran matakan tsaro.

“’Yan bindiga sun yi wa tsarin tsaron NDA kutse a safiyar nan inda suka shiga cikin barikin da ke yankin Afaka suka kashe sojoji biyu suka kuma yi garkuwa da daya,” inji shi.

Ya kara da cewa, “Kwalejin, da hadin gwiwar Babbar Runduna ta 1 ta Sojin Kasa da kuma Rundunar Horo ta Sojin Sama da sauran hukumomin tsaro da ke Jihar Kaduna na bin masu garkuwar a yankin domin kubutar da wanda aka yi garkuwa da shi.”

– Harin NDA: Ba farau ba

Harin NDA da aka yi garkuwa da Manjon shi ne na biyu a yankin na Afaka da ’yan bindiga suka kutsa cikin kwaleji suka yi garkuwa da mutane.

Kafin Harin NDA, ’yan bindiga su taba kutsawa cikin Kwalejin Gandun Daji ta Tarayya da ke yankin da tsakar dare suka yi awon gaba da dalibai, sai da aka biya kudin fansa suka sako su.

A lokacin lamarin ya zama abin magana, musamman ganin kusancin waccan kwalejin da NDA da Barikin Sojin Sama da Hedikwatar Soji ta Runduna ta 1 ta Sojin Kasa da Barikin Ribadu.

– Matakan tsaron NDA

Sai dai makwabtan NDA da ke yankin Afaka, inda ’yan bindiga suka suka yi garkuwa da dalibai 28 a watan Disamban 2020 ba su taba tunanin irin haka za ta faru da kwalejin sojojin ba.

Baya ga tsauraran matakan tsaro duk daga kofar shiga, NDA na zagaye ne da katangar kankare ta kowace kusurwa; ga kuma dakaru da ke yawon sintiri a zagayen katangar a tsawon dare.

A shekarun baya ne aka dauke matsugunin kwalejin daga tsohuwar tsangayarta da ke Babban Barikin Sojoji na Ribadu, wanda ke zagaye da unguwannin farar hula, zuwa yankin Afaka da ke Mando.

Ana ganin sauya wa matsugunin wani mataki ne na kare shi daga yiwuwar kutse da kuma sama wa kananan hafsoshin da ake horarwa natsuwa.

A halin yanzu, hatta babura masu kafa uku da ke jigilar fasinja, NDA na da nata.

Daga babbar kofar shiga harabar, inda mutum zai iske shingen bincike zuwa inda gine-gine suke akwai tafiya mai nisa.