✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya kamata ku sani kan shirin tallafin gwamnati na Survival Funds

Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa a ranar Litinin, 21 ga watan Satumbar 2020 za ta bude shafin rijistar tallafinta na kanana da matsakaitan sana’o’i.…

Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa a ranar Litinin, 21 ga watan Satumbar 2020 za ta bude shafin rijistar tallafinta na kanana da matsakaitan sana’o’i.

Kudaden tallafin dai da aka yi wa lakabi da Survival Funds kyauta ne ba rance ba, kuma an kirkiro shirin ne da nufin tallafawa masu karamin karfi da ke da kananan da matsakaitan sana’o’i domin su samu su farfado daga radadin annobar COVID-19.

Ana sa ran raba tallafin da yawansa ya kai kimanin Naira biliyan 75 ga akalla masu sana’o’i miliyan daya da dubu dari uku a duk fadin kasar, yayin da akalla mutum 35,000 za su amfana da shi daga kowacce jiha.

Za a bai wa mutane 250,000 damar yin rijista da zarar an bude shafin a a ranar Litinin da dare.

Wani mai sana’ar sayar da kayan miya
Hoto: BBC

Su wa ye su ka cancanta su ci gajiyar tallafin?

  • Wanda ya kasance mai karamar sana’a ko kasuwanci ko kuma wanda ya ke zaman kansa.
  • Kaso 45 cikin 100 na wadanda za su amfana za su kasance mata ne, kaso biyar kuma masu bukata ta musamman.
  • Idan kuma kamfani ne da kai, dole ka kasance kana da rijista da Hukumar Yi wa Kamfanoni Rijista (CAC), kana da akalla ma’aikata uku wadanda shugabansu zai kasance dan Najeriya ne kuma yana da lambar shaidar ajiy a banki ta BVN.
  • Ga masu zaman kanus kuwa, ana bukatar masu sana’o’i kamar na harkar sufuri, direbobin tasi da bos-bos, kanikawa da dai sauransu.
  • Masu sana’o’i irinsu ayyukan famfo, birkiloli, masu aikin wutar lantarki da sauransu.
  • Za a bayar da fifiko ga jihohin Legas, Kano da kuma Abiya.

Yadda za ku yi rijista domin neman tallafin

Daga ranar Litinin, 21 ga watan Satumbar 2020 da misalin 10 na dare ne za a bude shafin intanet domin fara yin rijistar shirin.

Da zarar an bude shafin, masu sha’awa za su iya ziyartarsa a www.survivalfund.ng inda za a sami karin bayani da kuma yin rijistar.