✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abokai sun tara wa mawaki Davido sama da N100m cikin yini daya

Abokn mawakin dai sun fara turo masa kudaden ne bayan salon da ya wallafa a shafinsa na Instagram.

Abokai da masoya sun tara wa mawakin Kudu, David Adeleke wanda aka fu sani da Davido sama da Naira miliyan 100 a yini daya.

Lamarin wanda aka fara da wasa, ya zama abin magana a kafafen sadarwa.

Mawakin ne ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa, “Muna samun daukaka ne idan muna taimakon wasu ko? To tunda na taimaka wajen daga wasu a shekaru da dama a baya, nima yanzu ina son ganin asalin abokaina. Dukan abokaina ina so su aiko min da Naira miliyan 1. An ce mu ne kungiyar Biliyan 30. Idan ba ka turo ba, ba ka cikinmu.”

Daga nan ne kuma ya kira abokan aikinsa su Mayorkun da Perruzzi da Dremo da Don Jazzy da sauransu.

Nan sai ya ajiye asusun ajiyan bankinsa, inda a cikin kankanin lokaci aka tara makudan kudade.

A lokacin hada wannan labarin, an samu Naira miliyan 122 kamar yadda Aminiya ta gani.

Daga cikin wadanda ya ce sun tura kudaden akwai Femi Otedola da Emeka Okonkwo da Obi Cubana da sauransu.