✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abokin mahaifi ya yi wa ’yar shekara 13 fyade a Nasarawa

Mutumin ya yi lalata da ita ne bayan ya kira da zummar zai aike ta.

Hukumar Tsaro ta NSCDC ta sanar da kama wani dan shekara 20 kan zargin yi wa yarinya mai shekara 13 fyade a Jihar Nasarawa.

Kakakin NSCDC reshen jihar, DSC Jerry Victor ya ce mutumin da ya yi wa yarinyar fyade ya sanya ta samu juna biyu a Lafiya, babban birnin jihar.

Haka kuma, NSCDC ta ce ta kama wasu mutum biyu daban da zargin lalata da wata ’yar shekara 13.

Da yake gabatar da su a gaban ’yan jarida, DSC Jerry Victor, ya ce an kama mutanen ne a wurare daban-daban na jihar.

“Wadanda ake zargi sun amsa laifinsu na yi wa yarinyar mai shekara 13 fyade,” a cewarsa.

Ya kara da cewa daya daga cikin wadanda ake zargi da yi wa yarinyar fyade abokin mahaifinta ne.

Yarinyar ta shaida wa Aminiya cewa mutumin ya yi lalata da ita ne bayan ya kira da zummar zai aike ta.