✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abokin takarar Tinubu na wucin-gadi ya janye

Akwai wurare da dama da zan iya yi wa APC aiki da kwazo.

Alhaji Kabiru Ibrahim Masari, ya sanar da janyewa daga takarar kujerar Mataimakin Shugaban Kasa na jam’iyyar APC.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da ake faman cece-kucen cewa jam’iyyar ta tsayar da tsohon gwamnan Jihar Borno, Kashim Shettima a matsayin tsayayyen dan takararta na Mataimakin Shugaban Kasa.

Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar Juma’a, 17 ga watan Yuni ne jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, ta mika sunan Alhaji Masari wanda jigon dan siyasa ne a Jihar Katsina, a matsayin wanda zai yi wa Asiwaju Bola Tinubu abokin takarar Shugaban Kasa na wucin gadi.

Sai dai cikin wata wasika da ya fitar a Lahadin nan, ya sanar da jam’iyyar janyewarsa daga takarar wannan mukami bayan ganawa da tsohon gwamnan na Jihar Legas.

“Ina mai sanar da Shugabannin jam’iyyarmu a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari, wannan shi ne sakamakon tattaunawar da na yi da dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu.

“Na janye daga wannan takara amma ina da yakinin cewa akwai wurare daban-daban da zan iya bai wa jam’iyyar da kasa baki daya gudunmuwa gwargwadon hali.”

Ana iya tuna cewa, jam’iyyar APC ta tsayar da Tinubu a matsayin dan takararta na kujerar Shugaban Kasa yayin Babban Taronta na zaben fitar da gwani da ta gudanar a tsakanin ranar 7 zuwa 8 ga watan Yunin da muke ciki.

Sai dai tun daga wannan lokaci, jam’iyyar ta gaza cimma matsaya, inda ta rika fadi-tashin ganin ta zabi abokin takarar Tinubun amma hakarta ba ta cimma ruwa ba har zuwa lokacin da wa’adin mika sunayen ’yan takara ga Babbar Hukumar Zabe ta kasar ya cika.

A yayin da wa’adin ke cika ne jam’iyyar ta mika sunan Alhaji Masari a matsayin wanda zai yi wa Bola Tinubu abokin takarar Shugaban Kasa na wucin gadi.