✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abu 3 da suka hana Najeriya magance matsalar tsaro —Amurka

Wadannan miyagun ababe sune suka hana jami'an tsaro gudanar da ayyukansu.

Kasar Amurka ta ce cin hanci da rashawa da rashin aiwatar da hukuncin da ya dace daga bangaren shari’a na daga cikin matsalolin da suka haifar da koma baya a sha’anin tsaron Najeriya.

A cewarta, wadannan miyagun ababe su ne suka jawo kama-karya tsakanin jami’an soji da ’yan sanda da kuma ’yan sandan farin kaya da ke aiki a Najeriya, abinda ke hana su gudanar da ayyukansu kamar yadda aka saba.

Wani rahoto da gwamnatin Amurka ta gabatar wanda ya mayar da hankali a kan take hakkin Bil Adama a shekarar 2021, ya duba batutuwa da dama da suka hada da dangantaka tsakanin hukumomin da fararen hula da kare hakkin Bil Adama da cin hanci da rashawa a hukumomin gwamnati da dama da kuma kama karyar da ake samu a tsakanin jami’an tsaro.

Amurka ta bayyana cewar cin hanci da rashawa tsakanin jami’an gwamnati da kuma bangaren shari’a ya haifar da kama karya a cikin kasar, kuma ya zama babban kalubale a tsakanin jami’an tsaro, musamman ’yan sanda da soji da kuma ’yan sandan farin kaya.

RFI ya ruwaito rahotan yana cewa duk da yake ’yan sandan da soji da kuma ’yan sandan farin kayan na da shugabannin fararen hula, lokaci zuwa lokaci suna yin gaban kansu wajen gudanar da wasu ayyukan da suka saba ka’ida ba tare da sanin magabatansu ba.

Amurka ta ce wadannan jami’ai kan yi amfani da karfi wajen tarwatsa masu zanga-zangar lumana da kuma kama wadanda ake zargi da aikata laifuffuka, yayin da ta zargi ’yan sanda da amfani da karfin da ya wuce kima wajen gudanar da irin wadannan ayyukan nasu.

Rahotan ya ce take hakkin Bil Adama da cin hanci da rashawa da kashe mutane ba bisa ka’ida ba na ci gaba da zama abin damuwa a kasar, sakamakon rahotannin da ake samu dangane da karuwar matsalar daga ’yan Najeriya.