✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ABU Zariya ta sallami ma’aikatan wucin gadi

Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya ta sallami ma’aikatanta na wucin gadi. Hukumar ABU ta ce sallamar ta fara aiki ne dagar ranar Litinin…

Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya ta sallami ma’aikatanta na wucin gadi.

Hukumar ABU ta ce sallamar ta fara aiki ne dagar ranar Litinin 15 ga watan Yunin da muke ciki.

Sanarwar da Ramatu Mohammaed ta fitar a madadin Rijitaran makarantar ta ce sallamar ta shafi dukkan malamai da ke zuwa daga wasu makarantu da ma’aikata da ake sabunta kwangilarsu wata-wata.

Sai dai sanarwar hukumar jami’ar ba ta yi bayanin game da dalilin sallamar ma’aikatan da abin ya shafa ba.

Idan dai za a iya tunawa, ko a makon da ya gabata sai da Jami’ar Bayero dake Kano ita ma ta dauki makamancin wannan mataki, kamar inda tsarin biyan albashi na IPPIS ya tanadar.