✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubuwa 20 da ya kamata ku sani game da Sheikh Dahiru Bauchi

Ga wasu abubuwa da ba kowa ya sani ba game da shi

A farkon watan Almuharram ne fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, kuma jigo a Darikar Tijjaniyya a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya cika shekara 98 a duniya.

Baya ga tarin iliminsa da yawan shekaru, akwai wasu tarin baiwa da Allah Ya ba malamin, wadanda ba kowa ne ya san da su ba.

 

Aminiya ta yi nazari a kansu, inda ta zakulo muku abubuwa 18 da ya kamata ku sani a kansa.

Ga wasu daga ciki:

  1. Ya fi kowa yawan zuri’ar da ta haddace Alkur’ani a duniya, inda yake da ’ya’ya da jikoki da tataba-kunne kusan 300 da suka haddace Alkur’ani mai girma
  2. Kundin tattara bayanai na Cholan Book Of World Records, ya ba shi shaidar girmamawa saboda yawan zuri’a mahaddata
  3. Yana da ’ya’ya 95
  4. Yana da jikoki 406
  5. Yana da tattaba-kunne 100
  6. ’Ya’yansa mahaddata Alkur’ani 77
  7. Jikokinsa mahaddata Alkur’ani 199
  8. Tattaba-kunnensa mahaddata Alkur’ani 12
  9. Shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Koli da ke bayar da fatawa a addinin Musulunci a Najeriya
  10. An haife shi a watan Janairun 1927, wanda ya yi daidai da watan Muharram 1346 Bayan Hijira
  11. A ranar Laraba aka haife shi a a garin Nafada da ke Jihar Gombe a yanzu
  12. Kwararre ne a fannin Alkur’ani da Tafsiri da Ma’arifa da Hadisi da Harshen Larabci da Li’irabi da Fikihu
  13. Jami’ar Tarayya da ke Lafiya a Jihar Nasarawa ta ba shi Digirin girmamawa
  14. Gwamnatin Najeriya ta ba shi lambar girmamawa ta kasa ta OFR
  15. Ya musuluntar da dubban mutane
  16. Yakan yi saukar Alkur’ani duk bayan kwana biyu
  17. Mutane fiye da 140,924 suka haddace Alkur’ani a makarantunsa da ke fadin Najeriya
  18. Ya kafa makarantun haddar Alkur’ani sama da 1,500 a Najeriya da wasu kasashen Afirka
  19. Karkashin gidauniyasa, an gina dakunan karatu guda 133,060 a Arewacin Najeriya
  20. Ya shafe shekaru sama da 50 yana gabatar da tafsirin Alkur’ani a cikin watan Ramadan