✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubuwa 6 game da Farouk Lawan

An daure shi ne bayan samunsa da laifin karbar rashawa daga Femi Otedola.

Farouk Lawan, tsohon dan Majalisar Wakilai wanda aka yanke wa hukunci daurin shekara bakwai a gidan yari ranar Talata, sanannen suna ne a zauren Majalisar Wakilan tarayya.

Bayan shafe shekara takwas ana tafka shari’a, daga karshe dai wata babbar kotu a birnin tarayya da ke Abuja, ta yanke hukunci a kan shari’ar da ta shafi cin hanci da rashawa da aka yi wa tsohon dan majalisar, wanda ake yi wa lakabi da ‘Mai Nagarta da Gaskiya.’

An daure shi ne bayan da aka same shi da laifin karbar rashawa daga attajirin dan kasuwar nan Femi Otedola, a lokacin binciken badakalar kudaden tallafin mai a 2012.

Femi Otedola ya zargi Lawan din da neman a ba shi Dala miliyan uku domin cire kamfanin mai da iskar gas na Zenon Petroleum and Gas Limited, daga jerin kamfanonin da ake bincikar su a lokacin.

Ga abubuwa guda shida da ya kamata ku sani game da Farouk Lawan:

Rayuwarsa

An haifi Farouk Lawan a ranar 6 ga Yulin 1962 a Karamar Hukumar Shanono da ke Jihar Kano. Ya girma a Kano inda ya yi karatun firamare da sakandare har ma da gaba da sakandaren a can.

Aikinsa

Ya yi digirinsa na farko a Jami’ar Bayero da ke Kano, indaya fara aiki a zaman Rajistira a Kwalejin Fasaha ta Jihar Kano. Daga baya ya shiga siyasa inda ya yi suna sosai a fagen.

Shekara 16 a matsayin dan majalisa

Ya fara shiga fagen siyasar ne a 1999 lokacin da ya yi takarar kujerar dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Bagwai da Shanono a zayren majalisar tarayya karkashin Jam’iyyar PDP.

Ya kasance a zauren har na tsawon shekara 16 daga 1999 zuwa 2015. Ya sha kaye a karon farko a hannun Sule Aliyu Romo.

Tarihin lakabin da ya samu na Mai Gaskiya da Nagarta

Ko shakka babu Farouk Lawan ya zama wanda muryarsa ta fi amo a zauren Majalisar Wakilan kafin badakalar da ta shafe shi a 2012.

Ya kasance jarumi marar tsoro wanda ba a nuku-nuku da shi, wadannan sun sanya shi ya samu daukaka a zauren inda aka lakaba masa sunan ‘Mai Gaskiya da Nagarta’.

Ya jagoranci tsige Patricia Etteh

Ya jagoranci gangamin da ya tilasta Kakakin Majalisar mace ta farko, Patricia Eteh, ta yi murabus a 2007. Gungun ’yan majalisar da ya jagoranta ya zargi Eteh da kashe Naira miliyan 620 ba bisa doka ba wajen gyaran gidanta tare da bayar da kwangiloli ga ’yan kanzaginta.

Yadda ya samu kansa a badakalar har ya karkare a fursuna

A 2012, ya jagoranci Kwamitin Majalisar wanda ya binciki tallafin man da Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayar. An kafa kwamitin bayan zanga-zangar da ta biyo bayan cire tallafin man da gwamnatin Goodluck Jonathan ta yi.

A cikin rahoton, kwamitinsa ya ce ya bankado badakalar kudade a harkar tallafin man fetur. Rahoton ya ce an biya tallafin Dala miliyan 6.8 na man da ba a ma shigo da shi kasar ba.

Farouk Lawan, ya samu kansa a aikata rashawar ne a yayin da yake bincikar kamfanonin da ake zargin suna da kashi a gindinsu a badakalar tallafin man.

Wani faifan bidiyo ya nuno shi yana karbar Dala 500,000 domin cire kamfanin Femi Otedola a cikin rahoton gabanin a gabatar da shi gaban zauren majalisar.

A yayin shari’ar, Otedola ya kafe cewar an kitsa bai wa Lawan rashawar da nufin bankado cin hancin da dan siyasar yake yi kuma da sanin Hukumar Tsaro ta SSS aka nadi bidiyon.

Sai dai shi ma Farouk Lawan din duk da ya yarda ya karbi kudaden amma ya nace kan cewa ya karba ne da niyyar ya kwarmata rashawar da dan kasuwar ya ba shi kuma ya tabbatar wa zauren majalisar cewa kwamitinsa ya fuskanci matsin lamba sosai yayin binciken.

Sai dai cikin shekara takwas da ya yi ta kai komo zuwa kotuna daban daban domin wanke kansa, a karshe Mai Shari’ah Angella Otaluka ta same shi da laifuka uku sannan ta yanke masa hukunci ranar Talata.