✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abun da ya kamata ku sani kan Ranar Hausa ta Duniya

Ranar Laraba 26 ga watan Agusta na wannan shekara ita ce “Ranar Hausa” ta duniya. A wannan rana ce ake baje-kolin fasahar harshen Hausa, da…

Ranar Laraba 26 ga watan Agusta na wannan shekara ita ce “Ranar Hausa” ta duniya.
A wannan rana ce ake baje-kolin fasahar harshen Hausa, da tattaunawa kan kyawawan al’adun Hausawa, da tunawa da tarihin kasashen Hausa musamman kafin zuwan Turawan Ingila.
Awannan rana ce ake neman kowa ya fito ya fadi albarkacin bakinsa kan abubuwan da suka shafi harshe da al’ummar Hausa, a kafafen sadarwa irinsu radiyo, talbijin, jaridu, mujallu, da shafukan intanet, da kafafen sadarwa na zamani.

An fara bikin Ranar Hausa ne a shafukan Facebook da Twitter a shekarar 2015, amma sai a shekarar 2016 ce ranar ta fara samun shahara a wajen masana da masu amfani da harshen Hausa, har ma da masu sha’awar yare da al’adun Hausawa.

A shekarar da ta gabata, Ranar Hausa ta samu babban tagomashi, a inda aka fara yin bikin ranar a wajen intanet, ta inda aka shirya tarurruka a garuwan Najeriya da ma kasashen ketare. Rahotanni sun nuna cewa an gudanar da bukukuwan Ranar Hausa a kasashe 11, da jihohin Najeriya sama da goma a shekara ta 2019.

#RanarHausa daya ce daga cikin jigon Kungiyar Mawallafa a Intanet ta Arewacin Najeriya (wato Bloggers Association of Northern Nigeria (BANN), wadda dama kungiya ce ta mutane masu kishin harshen Hausa da kuma cigaban Arewacin Najeriya.

Kungiyar ta dauki aniyar samar da wallafe-wallafe kan intanet cikin harshen Hausa da ma sauran harsunan Arewa, karkashin turbar ’yancin fafin albarkacin baki.

BANN na da manufar jan akalar ra’ayoyin duniya ne kan labarai da rahotanni game da al’ummar Hausa da Arewacin Najeriya.

Kungiyar BANN tana taya al’ummar Hausawan duniya murnar zagayowar bikin wannan rana.

Bikin #RanarHausa ya kasance daya daga manyan abubuwan da wannan kungiya ta samar tsawon kafuwarta na kimanin shekara shida.

An kafa kungiyar BANN ce a shekarar 2014, a lokacin da ake kiran ta da “Arewa Bloggers Forum”, wato Zauren Mawallafan Intanet ta Arewa.

Kungiyar ta kafu ne kan manufar inganta labarai da kuma batutuwan da ake tattaunawa kan kafofin sadarwa na zamani, da suka danganci Hausa da Arewacin Najeriya baki daya.

Daga cikin wadanda suka kafa kungiyar akwai Bashir Ahmad, wanda a yanzu daya daga cikin masu bai wa Shugaban Najeriya shawara ne.

Akwai kuma Jamila Kabiru Fagge, wadda tsohuwar ma’ikaciyar VOA Hausa ce, sannan akwai Abdulbaqi Jari, wanda ma’aikacin BBC Hausa ne a halin yanzu.

Sannan akwai Salihu Tanko Yakasai, na hannun-daman Gwamnan Kano da Malam Faisal Abdullah Ismail, Mudirin Jaridar Hausapedia, da Suleiman Garba Sule, Mudirin Jaridar Hausa Trends sai Ila Bappa Zaria Shugaban Jaridar Message Arewa, da kuma Hajiya Maryam Ado.

Gagarumin tasirin bikin Ranar Hausa wajen janyo hankalin duniya kan cigaban harshe da matsayin al’ummar Hausawa ta duniya, ya sanya masoya Hausa sun rungumi bikin hannu-bibiyu.

Sai dai kuma an samu wani rukuni na masu ganin su ne gatan harshen Hausa da yunkurin wuce-gona-da-iri wajen ikirarin cewa su suka kirkiri Ranar Hausa.

Amma abun mamaki shi ne kowannensu yakan ce ne ya kirkiri ranar a shekarar 2015, wato don ya yi daidai da ranar da Kungiyar Arewa Bloggers Forum ta kafa ainihin Ranar Hausa.

Ana iya binciken manhajar Twitter don duba wallafe-wallafen da ’yan Kungiyar BANN suka yi a shekarar 2015, don tabbatar da gaskiyar batun.

Yayin da babu wasu mutane ko kungiya da za su iya kawo rahoto ko labarin inda suka yi bikin Ranar Hausa kafin BANN ta fara kaddamar da ranar a 2015.

Sai dai wannan cikas bai tsole idon kungiyar Arewa Bloggers Forum, wadda yanzu ta koma Bloggers Association of Northern Nigeria ba.

A halin yanzu kungiyar ta mai da hankali wajen fadada yawan masu shigowa a dama da su wajen bikin wannnan rana.

Kuma tana maraba da duk mai son shirya taro kan ranar, ba sai lallai da izininta ba.

Kamar yadda aka saba duk lokacin bikin Ranar Hausa, masu amfani da kafafen sadarwar zamani irinsu Twitter, Facebook, da Instagram suna nuna basirarsu wajen kawo karin magana, zaurance, tarihi, da hotunan wuraren tarihi, da bidiyon wakokin Hausa, da kade-kade, da raye-rayen Hausa, da yada makalun da suka shafi Hausa.

A bana, kungiyar BANN ta fi ba da fifiko kan #MatasanZamani, wato #HausaMillenials, a matsayin babban maudu’in Ranar Hausa ta wannan shekarar.

Ku bibbiyi tattaunawa kan bikin Ranar Hausa ta bana.

Kungiyar BANN na gayyatar kowa da kowa bikin Ranar Hausa a duk inda ake gudanarwa a fadin duniya.

Sa’annan BANN na kiran mutane su nuna bajintarsu kan harshen Hausa a shafukan sadarwar zamani ta hanyar amfani da hashtag din #RanarHausa da takenmu na bana #MatasanZamani.

Kuma kuna iya ambaton adireshin BANN na Twitter, Facebook da Instagram, wato @BANNigeria, ko kuma shafinmu na yanar-gizo www.bannigeria.org

Mazhun Idris, a madadin kungiya. [email protected]