✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abun fashewa ya kashe mutum 4 A Fadar Sarki gabanin ziyarar Buhari a Kogi

Abun fashewan ya yi bindiga ne a Fadar Ohinoyi na Masarautar  Ebira, Dokta Ado Ibrahim

Mutum hudu sun rasu bayan wani abun fashewa ya yi bindiga gabanin ziyarar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a Jihar Kogi a safiyar Alhamis.

Rahotanni daga jihar sun ce abun fashewan ya yi bindiga ne a Fadar Ohinoyi na Masarautar  Ebira, Dokta Ado Ibrahim.

Majiyarmu ta ce, “Mutum hudu sun mutu,” sakamakon bindigar da wata transfomar wutar lantarki ta yi.

Shaidu sun bayyana wa Aminiya cewa abin fashewan ya tashi ne da misalin karfe 9 na safiyar Alhamis.

Abin ya faru ne a yayin da ake dakon ziyarar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zuwa Jihar Kogi a ranar.

Kawo yanzu dai hukumomin jihar ba su fitar da sanarwa game da lamarin ba.

Karin bayani na tafe…