✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abun fashewa ya yi kisa, ya jikkata mutane a Kogi

Wannan dai na zuwa ne makonni kadan bayan samun makamancin haka a garin Kabba

Rahotanni na nuna an samu mutuwar mutum guda, a Okene da ke Jihar Kogi, sakamakon fashewar wani abu da ba gano ko mene ne ba.

Aminya ta gano ce fashewar abin ta faru ne a daren ranar Alhamis a unguwar Idoji da ke Okene, yayin da mutanen unguwar suka taru domin bikin shekara na al’ada na Echane.

Wani wanda abin ya faru a kan idonsa mai suna Usman Animuko ya ce a abin fashewar ya nakasa wasu mazauna unguwar, inda wani mutum ya rasa kafafunsa, sannan wasu da dama sun samu rauni.

Haka zalika ya ce zuwa yanzu wanda ba gano sunansa ba ya rasu a hanyar kai shi Babban Asibitin Okengwe domin ba shi agajin gaggawa.

To sai dai dukkanin wadanda aka kai asibitin sakamakon lamarin an maida su Asibitin Lokoja, saboda babban asibitin garin da aka kai su babu wadatattun kayan aikin ba su kulawa.

Wannan dai na zuwa ne makonni kadan bayan samun makamancin haka a garin Kabba inda wata mata da kuma kaninta suka rasa rayukansu.

Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kogi, Edward Egbuka, ya ce yanzu haka kwararru kan harkar bam na wurin da abin ya faru domin gano musabbabin lamarin.