✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Acaba ta fara dawowa Kano saboda yajin aikin ’yan Adaidaita Sahu

Shekara tara kenan da haramta sana’ar acaba a Jihar.

A daidai lokacin da yajin aikin ’yan Adaidaita Sahu ya shiga rana ta biyu a Jihar Kano, da alama ’yan acaba sun fara kwararowa birnin, shekara tara bayan an haramta sana’ar a Jihar.

Yajin aikin dai wanda aka fara ranar Litinin, ya kawo tsaiko ga ilahirin harkokin sufuri, inda mutane suka koma neman mafita domin zuwa wajen harkokinsu na yau da kullum.

A shekarar 2013 ne dai gwamnatin Jihar Kano ta sanar da haramta sana’ar acaba lokacin da hare-haren kungiyar Boko Haram suka yi tsanani a Jihar.

Aminiya ta rawaito cewa wannan shi ne karo na biyu da ’yan Adaidaita Sahun ke tsunduma yajin aiki a cikin kasa da wata 12.

Suna yajin aikin ne dai a kan wata doka ta Hukumar Kula da Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) da ta bukaci sabunta izinin tuki ga dukkan direbobin a kan N18,000 ga sababbi, sai N8,000 ga tsofaffi a kowacce shekara.

Aminiya ta lura cewa baya ga ’yan acaba, ana kuma amfani da motocin Kurkura da motocin da ba na haya ba wajen sufurin mutane, lamarin da yake zama wata babbar barazana ta tsaro.

Hukumar Kula da Ababen Hawa ta Jihar ta KAROTA ta ce akwai akalla baburan Adaidaita Sahu guda 60,000 a fadin Jihar.

Shugaban KAROTA, Baffa Babba Dan-Agundi, ya shaida wa Aminiya cewa direbobin baburan sam ba sa girmama dokokin hanya, kuma ba sa son biyan harajin nasu na yau da kullum.

Ya ce wannan ne makasudin da ya haifar da rashin fahimta tsakaninsu da gwamnatin.

“Gwamnati na yunkurin samar da mafita, saboda muna jin kamar an kyale harkar sufuri a hannun ’yan Adaidaita Sahu su kadai a Kano,” inji Baffa.

Ya kuma ce gwamnati ta dauki tsauraran matakai wajen dakile yajin aikin.

Sai dai Shugaban Hadaddiyar Kungiyar Direbobin Adaidaita Sahu na Jihar Kano, Sani Sa’idu Dankoli, ya ce matakin bai zo musu da ba-zata ba, saboda an sanar da shi mako biyu da suka wuce.

Sai dai ya ba da tabbacin cewa nan ba da jimawa ba za a sasanta tsakaninsu da gwamnatin.

“Mun fara tattaunawa da mutanenmu, musamman la’akari da cewa yawancinmu ba su da wasu hanyoyin neman abinci face wannan sana’ar. Saboda haka ta shafi kowa, muna ba da tabbacin cewa a karshen kwana na biyu za mu dawo,” inji shi.