✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Adadin mutanen da suka mutu a girgizar kasa a Afghanistan ya haura 1,000

Wasu 1,500 kuma sun sami raunuka

Rahotanni daga kasar Afghanistan na nuni da cewa yawan mutanen da aka tabbatar da rasuwarsu sakamakon wata mummunar girgizar kasa a yanzu ya haura 1,000.

Sashen Al’adu da Yada Labarai na gwamnatin Taliban a kasar ya kuma ce yawan wadanda suka jikkata ya haura 1,500.

Hukumomin kasar sun ce adadin mutanen da suka rasu da wadanda suka samu raunuka na iya karuwa, a sakamakon wannan girgizar da ta auku kafin wayewar garin ranar Laraba.

Kakakin gwamnatin Afghanistan, Bilal Karimci, ya ce, “An samu girgizar kasa mai karfi, wadda ta yi ajalin daruruwan mutane, ta jikkata wasu daruruwa, tare da rusa gidaje da dama a wasu yankuna hudu da ke Lardin Paktika.

“Muna kira da babbar murya ga hukumomin agaji da jinkai su tura jami’ansu nan take zuwa wuraren, domin takaita tsanantar bala’in.”

Jirage masu saukar ungulu na daukar marasa lafiya kuma sai zirga-zirga suke ta yi suna kwashe mutanen da abin ya shafa daga kauyukan yankin zuwa asibiti.

Girgizar kasar ta auku ne da misalin karfe 1:00 na daren Talata, wato karfe 9 na daren agogon GMT, a yankin da ke da tazarar kilomita 44 daga birnin Khost da ke Kudu maso Gabashin kasar Afghanistan.

Kusan duk shekara a kan samun girgizar kasa a Afghanistan, inda Hukumar Agaji ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana asarar rayuka 560 a duk shekara a dalilin girgizar kasa.

Alkaluman hukumar sun nuna a cikin shekara 10 da suka gabata, Afghanistan ta yi asarar rayuka akalla 7,000 a sakamakon iftila’in girgizar kasa.