✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Adadin wadanda ruwan sama ya kashe a Brazil ya karu

Ruwan da aka tafka na tsawon sa’o’i uku, yawansa ya yi daidai da ruwan sama na tsawon wata guda.

Akalla mutane 104 ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa da kuma zabtarerwar kasa a Brazil bayan an shafe tsawon lokaci ana shatata ruwan sama kamar da bakin-kwarya.

Lamarin ya auku ne a birnin Petropolis mai cike da wuraren kayatarwa da yawon bude ido kamar yadda hukumomin kasar suka bayyana.

Ma’aikatar Kashe Gobara ta ce jami’anta 180 da sauran ma’aikatan ceto ne ke aikin ceto a wurin da abin ya faru a tsaunukan Petropolis, inda aka binne sarkin Brazil na karshe Pedro II, mai tazarar kilomita 68 daga arewacin birnin Rio.

“An aike da tawaga ta musamman da motoci da jiragen ruwa domin gudanar da bincike da ceto mutanee,” inji sanarwar.

Majalisar birnin ta ayyana “dokar ta-baci” a yayin da aka yada hotuna gidaje da motocin da suka lalace a sakamakon ibtila’in.

Shaguna da dama sun cika makil da ruwa sakamakon ambaliyar da ta shafe titunan tsakiyar birnin Rio mai dimbin tarihi.

Bayanai na cewa, akwai yiwuwar samun karin mamata, ganin yadda alkalumansu ke ci gaba da karuwa sannu a hankali a daidai lokacin da masu aikin ceto ke ta kokarin nemo masu sauran numfashi.

Dimbin mutane ne dai ke ci gaba da makalewa a cikin laka da kuma tarin buraguzai.

Da farko an ce, ana fargabar kimanin mutane 300 sun bace sakamakon wannan ibtila’in na ranar Taklatar nan.

Masana sun bayyana cewa, ruwan da aka tafka na tsawon sa’o’i uku, yawansa ya yi daidai da ruwan sama na tsawon wata guda.