✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Adadin wanda guguwar Batsirai ta kashe ya karu zuwa 92 a Madagascar

Ana ci gaba da samun karin adadin mutanen da suka mutu.

Yawan mutanen da suka mutu a sakamakon mahaukaciyar guguwar Batsirai a kasar Madagascar ya karu zuwa mutum 92.

Kungiyoyin agaji a kasar sun tabbatar da cewa mutum 110,000 ne lamarin ya rutsa da su kuma yawancinsu sun jikkata, lamarin da ya sa suke neman agajin gaggawa.

Ofishin agajin gaggawa na kasar ya ce adadin mutanen da suka mutu a yankin Ikongo, inda matsalar tafi girma ya kai 71, yayin da wasu sama da 61,000 suka rasa muhallansu.

Wani dan majalisar da ya fito daga yankin, Brunelle Razafintsiandrofa, ya ce akasarin mutanen sun mutu ne sakamakon rushewar da gidajensu suka yi a kan su.

Majalisar Dinkin Duniya tare da kungiyoyin agaji sun fara kai kayan agaji ga mutanen da lamarin ya rutsa da su.

Kasar Faransa ta tura jami’an agajinta 60 domin taimakawa wajen samar da tsaftacaccen ruwan sha a kasar.

Lamarin da ya faru a ranar Litinin ya jefa al’ummomi cikin halin ni-’yasu, amma ana ci gaba da kai wa kasar dauki daga sauran kasashen duniya.