✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Adamu ya yi watsi da zargin cinikin kuri’a a Zaben Ekiti

Babu wanda ya kirkiri wannan zargin face wadanda suka sha kaye a zaben da ya gabata.

Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Sanata Abdulahi Adamu, ya yi watsi da batun sayen kuri’a da aka zargi jam’iyyar da aikatawa yayin zaben Gwamnan Jihar Ekiti da ya gudana a karshen mako.

Dan takarar APC, Biodun Oyebanji ne ya lashe zaben na ranar Asabar din da ta gabata da jimillar kuri’a 187,057.

Shugaban jam’iyyar na kasa ya yi fatali da zargin sayen kuri’ar ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Fadar Shugaban Kasa a Abuja, jim kadan bayan gabatar da sabon zababben Gwamnan Ekiti ga Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Litinin.

A cewar tsohon gwamnan na Jihar Nasarawa, babu wanda ya kirkiri wannan zargin face wadanda suka sha kaye a zaben da ya gabata.

Kazalika, ya yi kira ga ‘yan jarida da su daina barin fusatattun ‘yan siyasa suna amfani da su wajen lalata mutuncin kasa saboda manufofi na siyasa.

Da yake tofa albarkacin bakinsa game da zargin sayen kuri’a a zaben da ya lashe, Oyebanji ya ce shi da jam’iyyarsu ta APC babu wanda aka samu da hannu a badakalar cinikin kuri’a a yayin zaben.

Ya kara da cewa, nasarar da ya samu na da nasaba kokarin shugabancin APC na kasa da kuma himmar da aka bayar a lokacin yakin neman zabensa.

(NAN)