✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Adewole Adebayo: Farfado da manufofin Abiola a SDP

Adebayo wanda ake kira yaron MKO Abiola yana fatan ya farfado da ‘manufofin’ Abiola a zaben 2023.

A ranar 12 ga Yunin badi (2023), za a cika shekara 30 cif da zaben Shugaban kasa da ake dauka marigayi MKO Abiola wanda ya yi takara a karkashin Jam’iyyar SDP ya lashe.

A tarihin siyasar Najeriya, ba za a taba mantawa da wannan zabe ba, saboda yadda aka gudanar da shi a cikin gaskiya da adalci.

A wancan lokaci Mista Adewole Adebayo yana dan shekara 20, kuma dalibi a Jami’ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife, yana karantar fannin lauya.

A yanzu Adewole Adebayo shi ne dan takarar Shugaban kasa a zaben 2023, a karkashin Jam’iyyar SDP.

Adebayo wanda ake kira yaron MKO Abiola yana fatan ya farfado da ‘manufofin’ Abiola a zaben 2023.

Shin zai bayar da mamaki? Shin Adebayo yana da gogewar siyasar da zai dawo da ruhin Abiola a siyasa? Shin SDP kamar lokacin Abiola jam’iyya ce da take da karfi a Najeriya?

Wadannan tambayoyi suna da wuyar amsawa ga Adebayo nan take, inda ya bayyana manufarsa da cewa, “Za mu fara ne daga inda Abiola ya tsaya – Bankwana da talauci. Kuma saboda shekara 29 da suka gabata ana fama da rashin tsaro. Don haka muka ce: “Ban-kwana da talauci da rashin tsaro.”

Wane ne Adewole Adebayo?

An haifi Adewole Adebayo ne a ranar 8 ga Janairun 1972 a birnin Ondo, babban birnin Jihar Ondo. Ya yi makarantar firamare ta St. Stephen a Ondo daga 1978 zuwa 1983. Sai Kwalejin St Joseph da ke Ondo daga 1983 zuwa 1989. Daga nan ya tafi Jami’ar Obafemi Awolowo, inda ya yi digiri a fannin lauya. Ya zama kwararren lauya bayan kammala Makarantar Horar da Lauyoyi da ke Legas a 2000. Adebayo ya samu tafiya wata makarantar horar da lauyoyi da ke birnin New York, a kasar Amurka.

Hakan ya ba Adebayo lasisin yin aikin lauya a kasashen Amurka da Austireliya da Kanada da Ingila da kotunan biranen Kalifoniya da New York da kotunan tarayya na Amurka.

Ya fara aikin lauya ne a karkashin Tunji Abayomi and Co a birnin Legas. Bayan ya yi shekara biyu yana aikin lauya, sai ya kafa ofishinsa na aikin lauya mai suna Adewole Adebayo & Co a 2002. A 2016 ya kafa gidan talabijin mai suna

Bayan kasancewarsa lauya, Adebayo ya zuba jari a harkokin noma da magunguna da harkokin yada labarai.

Taimakonsa ga jama’a ya karade fannoni da dama kuma ya horar da matasa sama da 2000, kamar yadda abokai da mukarrabansa suka tabbatar.

Wani abokinsa da suka taso tun yarinta mai suna Dokta Remijius Friday Obinta ya ce, a kowane lokaci Adebayo yana nuna halayen shugabanci da aikata gaskiya da rikon amana da kuma tallafa wa matalauta da masu rauni.

Obinta tare suka yi sakandare da Adebayo, kafin su tafi Jami’ar Obafemi Awolowo, inda Adebayo ya karanta fannin lauya shi kuma Obinta ya karanta fannin tarihi.

“Yaron Abiola ne. Yana cikin kungiyar dalibai da suka yi gwagwarmayar yakin neman zaben Abiola da Kingibe. Ya yi imani da manufofin Abiola, don haka ya ce Jam’iyyar SDP ce ta dace da buri da manufofinsa ga kasar nan,” in ji Obinta, wanda babban malami ne a Sashen Tarihi na Jami’ar OAU.

Wani na kusa kuma mashawarci ga Adebayo mai suna Stephen Adewale ya ce, wannan dan takara nasu na Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar SDP mutum ne mai son tallafa wa matasa da samar masu da ayyukan yi.

Adewale da Adebayo sun sake hadewa ne a 2010, inda Adewale ya rubuta wata makala a mujallar harkokin wajen Najeriya, wadda shi (Adebayo) ya karanta yana can Amurka. “Yanzu na fi kusa da shi fiye da baya,” in ji Adewale wanda shi ne shugaban tashar talabijin ta da ke Ondo.

Ya ce, gidan talabijin na

da ke Ondo, daya ne daga cikin hanyoyin karafafa samar da aiki ga matasa tare da rainon taurarin a harkar watsa labarai.

“Shekara uku ke nan muna tafiyar da wannan tasha, ba tare da samun riba ba. Amma duk da haka a kowane wata muna biyan kowane ma’aikacinmu albashin akalla Naira 60,000,” in ji shi.

Daga tarihinsa za a fahimci Adebayo sabon yankan rake ne a fagen siyasa, don haka ba shi da kwarewa a fagen siyasa da shugabanci. Haka kuma a kasa irin Najeriya zai yi wuya ko ma ba zai yiwu ba wanda bai da kwarewar siyasa ya zama Shugaban kasa.

Bayan haka, har yanzu Adebayo na SDP yana fakewa ne a bayan Abiola shekara 29 bayan zaben 12 ga Yunin 1993. A yau jam’iyyar ba ta cikin manyan jam’iyyu hudu da ake jin dayansu ce za ta samu nasara a zaben badi. Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da Gidauniyar Anap Foundation ta tsara kuma NOI Polls Limited ta gudanar, ta nuna za a fafata zaben ne tsakanin ’yan takara hudu da ta ce Jam’iyyar LP ce za ta lashe, sai APC da PDP da kuma NNPP.

“Sakamakon ya nuna dukkan sauran ’yan takarar kuri’arsu ba ta taka kara ta karya ba,” in ji Gidauniyar Anap. ‘Manyan Manufofinsa’

A wajen Adebayo, hanya ta farko wajen magance matsalolin Najeriya ita ce, “mu gyara kanmu.”

“Abu na farko da ya wajaba mu yi shi ne mu gyara zukatanmu. Idan ba mu yi haka ba, sakamakon da za mu samu sai ya fi na 2019 muni.

“Abin da zan ce ga ’yan Najeriya shi ne abin da zan gaya wa bakaniken motata. Shin ka fahimci matsalar da ke damun motata? Idan ba mu fahimci matsalolin Najeriya ba, ba za mu iya gyara ta ba,” in ji Adebayo.

Ya kara da cewa: “Ina son in gyara kasar nan. Kuma sufanata ita ce gaskiya.”

Adebayo ya ce, ya gano maganin matsalolin Najeriya musamman talauci a sashe na biyu na kundin tsarin mulkin Najeriya.

Ya ce: “Farkon abin da zai fara yi shi ne kafa gwamnatin da ba za ta dada jawo talauci ba. Ta yaya za a kauce wa talauci? Shi ne a yi aiki da sashe na biyu na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, wanda ya zayyana yadda za rarraba kudade da sauran dukiya da albarkatun kasa da yadda za a ba wa kowane dan Najeriya dama.”

A wata hira da aka yi da Adebayo ya ce, a matsayin Shugaban kasa, zai karbi kowace irin shawara “ko da mai daci ce.”

“Ni mai karbar shawarwari ne. Hasali ma na fi son a rika ba ni shawara, kuma ina godiya ga Allah bisa yawan shawarwarin da ake ba ni. Zuciyata tana hana ni karbar muguwar shawara. Ina son kyakkyawar shawara, don haka ba na watsi da shawara.

“Ba na jin kamar an raina ni lokacin da aka ba ni shawara. Za ka iya ba ni shawara cikin izza. Idan kana da kyakkyawar shawara za ka iya rubutawa ka jefa min. Zan karanta ta, domin abin da yake da muhimmanci shi ne idan na yi abin kirki ni zan samu yabo,” in ji shi.

Dangane da tsare-tsaren da ya yi wa tattalin arziki, ya yi alkawarin fadada hanyoyin tattalin arzikin Najeriya maimakon dogaro da man fetur.

Da yake jawabi a wajen taron da aka shirya kwanakin baya a Cibiyar Tarihi ta Gidan Arewa da ke Kaduna ya ce, “Abin da ba mu iya tafiyar da shi yadda ya kamata ba shi ne siyasar man fetur. Muna kallon fetur ne ta fuskar siyasa.”

“Bari in gaya maku a cikin manyan albarkatun kasa 100 da muke da su, man fetur ba shi ne na farko ba. Me ya sa ba ma mayar da hankali a kan harkokin noma. Misali, a yankin kudancin Kaduna kadai da ake noman citta, idan aka kafa kamfanin sarrafa citta a wajen, za a rika samun Dala biliyan 1.4 duk shekara,” in ji shi.

Ya ce, a karkashin gwamnatinsa, za a bai wa kowace jiha damar ta kula da albarkatun yankinta.

Game da yadda zai magance rashin aikin yi kuwa ya ce, “Idan muka aiwatar da sulusin ayyukanmu, za mu samar da ayyukan yi miliyan 30, za a fara neman ma’aikata daga Ghna. Duk dan Najeriya zai samu aiki.”

Da yake magana kan cin hanci da tsantseni wajen tafiyar da gwamnati, lauyan ya ce, yana da dabarun da zai tunkari wannan matsala a Najeriya.

Ya ce, “Dabarun da zan yi amfani da su sun fi na hukumomin EFCC da ICPC. A lokacin su Sa Ahmadu Bello, babu EFCC da ICPC. ’Yan doka kawai suke da su, amma Sa Ahmadu Bello ba ya amfani da motar gwamnati idan ya koma gida bayan tashi daga aiki.

Ba abu ne mai wahala ba. Wadanda suka kirkiro EFCC da ICPC, sun kirkiro su ne domin yakar abokan gabarsu”, in ji shi.

Kan matsalar tsaro, Adebayo ya ce, “Zan yi amfani da karfin gwamnati wajen magance hare-haren da ake kai wa ‘yan Najeriya, don kawar da tunanin da wasu ke yi cewa Najeriya tana daf da rugujewa.”