Najeriya A Yau: AFCON 2021: Tana Kasa Tana Dabo | Aminiya

Najeriya A Yau: AFCON 2021: Tana Kasa Tana Dabo

    Halima Djimrao da Muhammad Auwal Suleiman

Domin sauke shirin latsa nan

Hankulan masoya kwallon kafa a Najeriya kamar na takwarorinsu a kasashen Afirka da ma wasu sassan duniya sun koma Kamaru, inda aka bude Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka 2021.

Kasashen Afirka 24 ne za su fafata a gasar, kuma tuni kasar Kamaru mai karbar bakuncin gasar ta kara da Burkina Faso a wasan da aka tashi 2-1.

Najeriya ma ta samu damar shiga gasar amma tana kasa tana dabo, saboda ma’abota kwallon kafa a kasar na ganin cewa da jan aiki a gaban ‘yan wasan Super Eagles.

A cikin shirin Najeriya A Yau, mun tattauna da masu sharhi a kan wasanni game da yadda suke kallon wannan gasa.