✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

AFCON 2021: COVID-19 ta kama ’yan wasa 12 a tawagar Tunisia

Hakan dai na nufin ba za su fafata wasan da kasarsu za ta buga da Najeriya ba.

A wani yanayi da ke zama koma baya, jiga-jigan ’yan wasan tawagar kasar Tunisia 12 a gasar cin kofin Nahiyar Afirka da ke gudana a Kamaru da kocinsu, Mondher Kebaier, sun kamu da cutar COVID-19.

Hakan dai na nufin ba za su samu damar fafata wasan da kasarsu za ta buga da tawagar Super Eagles ta Najeriya ba, wacce aka tsara yi a birnin Garoua ranar Lahadi.

Kasashen biyu dai za su kece raini ne a zagaye na biyu na gasar da ke gudana a kasar Kamaru.

A yayin wani taron manema labarai ranar Lahadi, mataimakin kocin tawagar ta Tunisia, Jalal Al-Qadri, ya ce akalla ’yan wasa 12 daga cikin tawagar ne suka kamu da cutar, kuma ba za su fafata wasan da Najeriya ba.

Hatta kocin kungiyar, Mondher, bai halarci taron manema labaran na ranar Asabar ba.

’Yan wasan da suka kamun sun hada da kyaftin din tawagar, Wahbi Khazri da Aissa Laidouni da Dylan Bronn da Ghaylène Chaalali da Ellyes Skhiri da Anis Ben Slimane da Mohamed Romdhane da Ali Maâloul da Ben Hmida da Aymen Dahmen Yoann Touzgha da kuma Issam Jebali.

Ya zuwa yanzu dai, tawagar Super Eagles ce kadai ba a taba yin nasara a kanta ba ko sau daya tun da aka fara gasar.