✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

AFCON 2021: Ivory Coast ta kora Aljeriya gida

Aljeriya ce kasa ta uku da aka cire daga gasar a matakin farko a gasar AFCON biyar da suka gabata.

Ivory Coast ta yi waje da Aljeriya mai rike da Kofin Kasashen Afirka daga gasar ta AFCON 2021 da ke gudana a Kamaru bayan ta casa ta 3-1 a birnin Douala.

Kafin wasan, da ma wajibi ne sai Aljeriya ta yi nasara sannan za ta samu damar wucewa zagaye na gaba na yan 16, amma tun kafin hutun rabin lokaci aka jefa musu kwallo biyu.

Franke Kessie ne ya fara cilla kwallo a ragar Aljeriya, sai kuma Ibrahim Sangare da ya ci ta biyu, kafin Nicolas Pepe ya zira ta uku.

Tauraron dan wasan Man City Riyadh Mahrez ne ya so zare wa Aljeriya kwallo daya a bugun fenareti amma ta bigi turke. Sai dai Sofiane Bendebka ya samu sa’ar farke wa Aljeriya kwallo daya a minti na 73.

A halin yanzu dai Aljeriya ce kasa ta uku da aka cire daga gasar a matakin farko a gasar AFCON biyar da suka gabata.

A jiya Laraba ne tawagar Super Eagles ta Najeriya ta shallake zuwa zagayen ’yan 16 bayan ta lallasa Guinea-Bissau da ci 2-0.