✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

AFCON 2021: Najeriya ta haye saman teburin Rukunin D bayan ta yi raga-raga da Guinea-Bissau

Super Eagles ta dare kan saman teburin rukunin D bayan lashe wasanninta gaba daya.

Tawagar ’yan wasan Super Eagles ta lallasa kasar Guinea-Bissau da ci 2-0 a wasan karshe na Rukunin D a matakin farko na Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirkta ta 2021.

Tawagar ’yan wasan kasashen biyu sun barje gumi ne a daren ranar Laraba, a filin wasa na Roumdé Adjia da ke kasar Kamaru.

An shafe minti 45 din farko ba tare da jefa kwallo a ragar kowace kasa ba.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne dan wasan Super Eagles, Umar Sadiq, ya zura kwallo a minti na 56.

Shi kuma Troost-Ekong, wanda shi ke rike da kambun Kyaftin din tawagar ya jefa kwallo na biyu a minti na 79.

Yanzu haka tawagar Super Eagles ce ke kan gaba a Rukunin D da maki tara, a yayin da kasar Masar ke biye mata a matsayi na biyu da maki shida.

Sudan ta kare a mataki na uku da maki daya, sai Guinea-Bissau, wadda ita ce ta karshe da maki daya.