✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

AFCON 2021: Senegal ta doke Cape Verde da 2-0

Senegal ta zura kwallaye biyu ta hannun ’yan wasanta Mane da Dieng.

Tawagar ’yan wasan kasar Senegal ta shiga zagaye na gaba, bayan ta doke takwararta ta Cape Verde da ci biyu ba ko daya.

Yayin wasan da aka doka a yammacin ranar Talata a filin wasa na Kouekong na kasar Kamaru, Senegal ta ciri tuta.

Hakan dai na nufin Cape Verde ta fice daga gasar cin kofin na nahiyar Afirka, bayan da aka ba ’yan wasanta biyu jan kati.

A minti na 21 da fara wasa aka ba dan wasan tsakiyar Cape Verde, Patrick Anderade, katin sallama sakamakon muguwar keta da ya yi wa dan wasan Senegal.

Bugu da kari, a minti na 57 aka ba mai tsaron ragar Cape Verde Vözinha jan kati, hakan ya sanya tawagar ’yan wasan kare wasan da ’yan wasa tara.

Sadio Mane ne ya fara zura wa Senegal kwallo a minti na 63, bayan shafe tsawon lokaci ya na kai hari.

A minti na 93, dan wasan gaban Senegal, Ahmadou Dieng, ya zura kwallo ta biyu a ragar Cape Verde.

Sai dai Cape Verde ta yi kokari sosai a wasan duk da samun jan kati da ’yan wasanta biyu suka yi, wanda bai hana su kai munanan hare-hare ga Senegal din ba.