✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

AFCON2021: A karon farko, Senegal ta daga Kofin Afirka

Senegal dai ta samu nasarar ne a bugun fenareti.

Tawagar Teranga Lions ta Senegal ta doke takwararta ta Masar a wasan karshe na Gasar Cin Kofin Afirka.

Senegal ta samu nasara ne a wasan bayan an yi bugun fanareti, inda Masar din ta barar da biyu.

Ke nan Sadio Mane ya yi nasara a kan abokinsa Mohamed Salah a karon battar da suka yi.

Wannan dai shi ne karo na farko da kasar ta Senegal ta taba daukar kofin, sabanin Masar din da ta lashe shi har sau biyar.